… Muna da kaset din batancin da ya yi kan dan Fodiyo – Matasan kadiriyya
Shugaban Shababul kadiriya na Jihar Sakkwato Malam Ahmad Sa’i ya ce sun yanke shawarar bin hanyar difilomasiyya ce don neman Sheikh dahiru Usman Bauchi ya janye kalamansa domin samar da sulhu ga mabiya darikokin biyu, amma sai suka ga malamin ya nemi su kawo hujja, “to abin da zangaya wa jaridar Aminiya shi ne a […]
Shugaban Shababul kadiriya na Jihar Sakkwato Malam Ahmad Sa’i ya ce sun yanke shawarar bin hanyar difilomasiyya ce don neman Sheikh dahiru Usman Bauchi ya janye kalamansa domin samar da sulhu ga mabiya darikokin biyu, amma sai suka ga malamin ya nemi su kawo hujja, “to abin da zangaya wa jaridar Aminiya shi ne a lokacin da na saurari bayanan da Sheikh dahiru Bauchi ya yi gudun kada na sanya kaina cikin kuskure, sai da na tashi na tafi gidan Shugaban Majalisar Sufayen darikar Tijjaniya na Jihar Sakkwato, Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal na kunna masa muryar Sheikh din daga farko har karshe, bayan ya gama saurare ya tabbatar min da muryar Sheikh dahiru Bauchi ce kuma a Abuja aka yi taron sai dai shi a lokacin taron ba ya kasar nan, daga nan ne muka yanke shawarar tuntubar jaridar Aminiya domin neman Sheikh din ya janye kalaman da ya yi kan dan Fodiyo wadanda ba su yi mana dadi ba.”
Malam Ahmad ya ruwaito kalaman Shaihin kamar haka: “Tajdidin Shehu dan Fodiyo aikinsa na addini ya kai Potiskum daga Sakkwato ? Ko Zuru bai kai ba. Akwai wani Sarkin Musulmi da aka taba yi, wani Gwamnan soja ritaya ya gina masallaci, Sarkin Musulmin wancan lokacin ya nemi cewa wai Musulmi (’yan Izala) sun ce a roke ka ka ba su masallacin, sai ya ce to ka zo ka yake ni ka ba mutanenka masallacin. Ko kakanka dan Fodiyo bai yaki garinmu ba nan Zuru. To Shehi Ibrahim ya hada duk duniya gaba daya, ba za mu yarda da Izala mu dawo karkashinta ba. Muna gaya wa dukkan ’yan Tijjaniya ba mu cikin wannan, ba za mu ajiye Sheikh Tijjani mu dauki Sa’ad Abubakar ba, shi ba shugabanmu ba ne, Sarkin Musulmin Izala ne, ba wani jagoranci da zai hada mu da Izala. ’Yan Tijjaniya a Najeriya ba ruwanmu da duk hadin kai da Izala. Ku gaya musu mu fa halifofin Sheikh Ibrahim ne, kuma a cikin malamai na kasar nan akwai ma jikan Annabi, in jikan Annabi yana wuri, jikan dan Fodiyo ko malami ne yana ja da shi, balle jikan dan Fodiyo jahili ne. In da kunya ai ba za a yi haka ba, ka ja mutane ka kai su wurin halaka, wurin tashin hankali, ba za mu yarda ba. Mu tsari na addini ba na siyasa ba ne, kuma ba wanda ya isa ya sanya mu dole kan wani abu.”
Shugaban Matasan kadiriyyar ya ce idan Sheikh dahiru Bauchi na da matsala da Sarkin Musulmi bai kamata ya sanya Shehu dan Fodiyo a ciki har ya ce tajdidinsa bai kai Potiskum ko Zuru ba.
“Wadannan kalamai da Sheikh dahiru Bauchi ya yi kan dan Fodiyo da Sarkin Musulmi ne muka nemi ya janye saboda samun maslaha, domin duk mutum yana kuskure,, mu a wurinmu cin mutuncin dan Fodiyo ne wadannan kalamai. Muna da muryarsa a jiye kuma in har yana ganin kage muka yi masa yana iya tafiya kotu domin neman hakkinsa,” inji Malam Ahmad.