‘Muna da ma’adanai 13 da za su maye gurbin man fetur’

A wani mataki na lalubo hanyar rage dogaro da arzikin man fetur a kasar nan, gwamnatin tarayya ta ce kasar nan na da ma’adanai akalla guda 13 wadanda za su iya mage gurbin man fetur, wanda farashinsa yake ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya. Ministan Kasuwanci da Zuba Jari Mista Olesegun Aganga ne ya […]

‘Muna da ma’adanai 13 da za su maye gurbin man fetur’
‘Muna da ma’adanai 13 da za su maye gurbin man fetur’

A wani mataki na lalubo hanyar rage dogaro da arzikin man fetur a kasar nan, gwamnatin tarayya ta ce kasar nan na da ma’adanai akalla guda 13 wadanda za su iya mage gurbin man fetur, wanda farashinsa yake ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya.

Ministan Kasuwanci da Zuba Jari Mista Olesegun Aganga ne ya bayyana hakan ne lokacin wani taro da daraktan hukumar kula da ma’adanai, Mista Olusegun Awolowo a Abuja. Ministan ya ce: “Wannan wani mataki ne shawo kan faduwar farashin danyen man fetur wanda kasar nan ta dogara da shi kacokan don samun kudin shiga,” inji shi.
Daga nan ya bayyana ma’adanan da za su maye gurbin man fetur din kamar haka: manja da koko da kashu da sikari da shinkafa da sauransu. Ya kuma umarci hukumar da ta yi duk abin da zai yiwu wajen ganin hakan ya tabbata nan ba da jimawa ba.