‘Muna da membobi sama da 35,000 a kungiyarmu’
Aminiya: Mene ne tarihin kafuwar wannan kungiya ta ku ta NATA kuma ta yaya kuka faro tafiyar da harkokin ta? Babu shakka kungiyar mu ta samo asali ne tun a shekara ta 1983, amma mu a Jihar Kano sai daga baya muka kafa reshen, yau kimanin shekara ashirin ke nan da aka fara gudanar da […]

Aminiya: Mene ne tarihin kafuwar wannan kungiya ta ku ta NATA kuma ta yaya kuka faro tafiyar da harkokin ta?
Babu shakka kungiyar mu ta samo asali ne tun a shekara ta 1983, amma mu a Jihar Kano sai daga baya muka kafa reshen, yau kimanin shekara ashirin ke nan da aka fara gudanar da ayyukan ta bisa jajircewar wasu mutane masu matukar kishin kasa da son ci gaban zamantakewa.
Aminiya: A matsayinka na shugaban kungiyar, wadanne nasarori za ka iya bayyanawa ka samar tun da ka karbi ragamar kungiyar NATA?
Gaskiya kafin in fara gutsura irin nasarorin da muka samu daga shigowa ta zuwa yau sai na yi godiya ga Allah madaukakin sarki wanda shine Ya taimake mu har muka samu gyaruwar al’amuran kungiya.
Da farko dai mun hade kan ’ya’yan kungiya tare da kara shigo da wasu cikinta wanda kafin zuwar mu, kananan hukumomi ashirin da biyu ne suke da tsarin shugabancin kungiyar a sassa arba’in da hudu amma yanzu muna da shugabanci a dukkanin kananan hukumomi arba’in da hudu a sassa dari da arba’in da hudu wanda hakan abin alfaharin mu ne baki daya.
Haka kuma kungiyar tana kara bullo da hanyoyi ingantattu na samar da karin gurabe na ayyuka dogaro da kai inda yanzu haka muka kafa wata kungiya mai karfi wadda ta kunshi kananan kungiyoyi goma sha uku domin bada horo kan sana’ar kanikanci da sauran ayyuka na dogaro da kai, don haka ina tabbatar da cewa nan gaba kadan ta karkashin kungiyar NATA za mu ci gaba da bullo da muhimman abubuwa domin kyautata rayuwar al’uma cikin yardar Ubangiji.
Aminiya: Ta yaya kuke samun kudaden tafiyar da kungiyar ta ku musamman ganin cewa ita kungiya tana bukatar kudi wajen gudanar da aikace-aikacen ta?
Muna samun kudaden tafiyar da aikin kungiyar ne ta hanyar karbar kudin kungiya na wata-wata inda muke karbar naira dubu daya daga kowane sashe cikin sassa dari da arba’in da hudu da muke da su a fadin Jihar Kano, sannan a ciki muke ware kaso da muke bai wa uwar kungiya ta shiyyar Arewa maso yamma ta yadda komai zai ci gaba da tafiya cikin nasara.
Bugu da kari, muna da kyakykyawar alaka tsakanin kungiyar NATA da gwamnatin Jihar Kano don haka ake ganin muna tafiya bisa fahimtar juna da aiki tare, domin ganin an hadu wajen rage yawan marasa aikin yi ta hanyoyi daban-daban kamar yadda kowa yake gani yanzu a jihar, fatan mu Allah Ya kara bamu zaman lafiya da kwanciyar hakali a wannan kasa tamu.
Aminiya: Ko me zaka ce dangane da shirin Gwamnatin Jihar Kano na tura matasa koyon gyaran mota a kamfanin fijo da ake yi?
Gaskiya wannan tsari ya yi kyau kwarai da gaske amma yana da kyau nan gaba gwamnati ta bamu damar ba da mutanen da za a kai wajen koyon gyaran saboda mune muka san duk wanda ya cancanci samun wannan dama. Sannan ina so inyi amfani da wannan dama wajen yin kira ga gwamnan Jihar kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ya bamu wata dama ta horar da matasa aikin kanikanci domin muna da kwararru da za su koyar kuma ba za a kashe abin da za a kashe a kamfanonin da ake tura matasan ba.
Muna so ne mu nuna wa gwamnatin Kano cewa mun kware ta fuskar gyaran ababen hawa da bada horo kan sanin makamar aiki cikin sauki da biyan bukata. Sannan muna kira ga masu iko da masu rike da mukamai na siyasa kamar ’yan majalisu da shugabannin kananan hukumomi da kamfanoni su rika tura mana mutane muna basu horo kan luggar gyaran ababen hawa ta yadda za a hada karfi wajen samar da abin yi ga dumbin matasan mu da ke zaune babu aiki.
Aminiya: Mene ne sakon ka ga masu ababen hawa da masu sayar da kayan gyara ganin cewa duk tafiyar daya ce?
Kafin in isar da sako na ga masu ababen hawa ko masu kayan gyara zai yi kyau in kara tunatar wa cewa dukkanin kanikawan da ke karkashin kungiyar mu ta NATA kwararru ne kuma masu rikon amana ne. Don haka ina tabbatar wa da masu ababen hawa cewa duk wanda ya kai gyaran abin hawansa wajen kanikawan NATA to zai samu biyan bukata kuma ina fata su kasu masu sayar da kayan gyaran kayan ababen hawa za su kara rike gaskiya da kaucewa bata sana’ar su wadda take da matukar muhimmanci.
Haka kuma ina kara jaddada godiyar mu ga Gwamnatin Jihar Kano saboda aiki tare da take yi wanda sakamakon hakan ake kara samar da guraben aiki ga matasa da ba su da abin yi, tare da fatan alheri ga shugabannin kungiyar mu ta NATA da kuma daukacin kanikawan kasar nan baki daya, kuma ina fata za a ci gaba da kokari wajen kare mutunci da martabar ita wanna kungiya tamu mai albarka.