Muna dab da hana shigo da kifi daga waje – Gwamnati

A sakamakon jan damara da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen bunkasa kananan manoma da kara musu kwarin gwiwa, ta ce za ta dakatar da shigo da kifi zuwa kasar nan da shekarar 2022. Ministan Gona da Raya Karkara, Alhaji Muhammadu Sabo Nanono ya bayyana haka yayin da yake karbar bakuncin shugabanin Kungiyar Masu Kiwon Kifi ta […]

Muna dab da hana shigo da kifi daga waje – Gwamnati

A sakamakon jan damara da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen bunkasa kananan manoma da kara musu kwarin gwiwa, ta ce za ta dakatar da shigo da kifi zuwa kasar nan da shekarar 2022.

Ministan Gona da Raya Karkara, Alhaji Muhammadu Sabo Nanono ya bayyana haka yayin da yake karbar bakuncin shugabanin Kungiyar Masu Kiwon Kifi ta Kasa (NFAN)  a karkashin jagorancin Dokta Gabriel Ogunsanya a Abuja.

Alhaji Sabo Nanono ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta gano tare da komawa ga harkar kiwon kifi gadan-gadan don wadata  kasa da fitar da shi zuwa kasashen waje, yunkurin da ya ce tuni gwamnati ta fara tsare-tsaren haka.

“Lokaci ya yi yanzu da za mu hada hannu wajen ganin mun bunkasa noman kifi a kasar nan. Dole mu tashi tsaye wajen rage adadin kifin da ake shigo da shi daga kasashen waje. A bara kawai mun bayar da lasisi  miliyan daya, amma na rage adadin zuwa rabi a bana.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Ministan yana cewa: “Fatarmu ita ce mu sake rage adadin bayar da lasisi ga masu shigo da kifi daga waje, don haka a badi ma zan sake rage adadin ta yadda nan da shekara biyu masu zuwa (2022) za mu dogara da kifin da muke samarwa,” inji shi

“A matsayinku na masu samar da kifin da ake amfani da shi ya kamata ku san hanyoyin bunkasa harkar domin nan da shekara biyu masu zuwa ba za mu sake yarda a shigo da kifi daga kasar waje ba. Duk da na san akwai masu cewa akwai nau’in kifin da ba ma kiwata shi a kasar nan musamman fararen kifi, amma iya wadanda ake kiwatawa ma kadai za mu iya amfana da su musamman labarin da na samu cewa su ma sun samu shiga da karbuwa a kasuwannin duniya. Don haka idan har kun kara kaimi kuka yi aiki tukuru za ku iya fitar da mu kunya a kasar nan,” inji shi.

Ya tabbatar wa kungiyar cewa gwamnati a shirye take wajen tallafa wa harkar tare da ba su tallafi.

Yayin da yake jawabi tun farko, Shugaban Kungiyar ta Kasa Dokta Gabriel Ogunsanya, ya yaba wa Ministan kan kokarin da yake yi wajen farfado da harkar noma a kasar nan. Sai ya mika kokon bararsu na a taimaka wa harkar kiwon kifi musamman a wasu fannoni da suka hada da horar da makiwata kifin da gabatar da su ga Babban Bankin Najeriya (CBN) da bankunan masana’antu da na noma don su rika kawo nasu daukin don bunkasa harkar a Najeriya.

Sannan ya bukaci Ministan ya duba hanyoyin farfado da harkar kiwon kifi da kasuwancinsa don tantance wurare da irin kifayen da ake samu a ko’ina a kasar nan.