Muna daukar matakai wajen kula da dabbobinmu – Shugaban Gidan Zoo na Kano
Alhaji Lawan Kenken shi ne Shugaban Gidan Zoo na Kano, a tattaunawarsa da Aminiya ya ce suna daukar dukan matakan da suka kamata wajen kula da dabbobin musamman zakuna. Shugaban ya ce a tsawon shekarun da gidan adana dabbobi ya kwashe ba a taba samun wata dabba ta fita daga cikin gidanta ba, ballantana ta […]

Alhaji Lawan Kenken shi ne Shugaban Gidan Zoo na Kano, a tattaunawarsa da Aminiya ya ce suna daukar dukan matakan da suka kamata wajen kula da dabbobin musamman zakuna.
Shugaban ya ce a tsawon shekarun da gidan adana dabbobi ya kwashe ba a taba samun wata dabba ta fita daga cikin gidanta ba, ballantana ta cutar da mai kula da ita ko jama’ar gari. “Ba mu wasa da duk abin da zai kawo mana cikas tun daga kan abincin dabbobin da kula da lafiyarsu,” inji shi.
Alhaji Lawan ya ce tun farko ba su danka aikin kula da dabbobi masu hadari sai a hannun mutane masu natsuwa. “Idan muka ga mutum mai rawar kai ko mai abubuwa da yawa a kansa to ba mu ba shi kula da dabbobi masu hadari. Aiki ne da yake bukatar natsuwa domin da zarar mutum ya tsalalke wani mataki to komai zai iya faruwa,” inji shi.
Ya ce Gidan Zoo na Kano ya yi fice a kasar nan “Mun bambanta da kowane gidan namun daji a kasar nan. Kana ganin dabbobinmu ka san lafiyayyu ne, akwai dabbar da in ka dauki mushen nama ka saka mata ko kallonsa ba za ta yi ba, saboda ta riga ta saba duk abin da za a ba ta ana ba ta bisa ka’ida. Muna da kwararrun likitoci da magungunan dabbobi masu inganci da kayan aiki da in matsala ta taso masu kula da dabbobin suna tare da kayan aikin dabbar ba za ta zo kusa da su ba, sai dai tsautsayi,” inji shi.