Muna Fargabar Za A Samu Hare-Hare A Wuraren Tarukan Jama’a — DSS

DSS tana fargabar za a samu harin ƙunar baƙin wake, ko kuma a dasa bam a wuraren tarukan jama’a.

Muna Fargabar Za A Samu Hare-Hare A Wuraren Tarukan Jama’a — DSS

DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta gargadi ‘yan Najeriya da ke faɗin kasar nan da su guji wuraren dandazon jama’a domin kauce wa barazanar harin ’yan ta’adda. 

DSS tana fargabar za a samu harin ƙunar baƙin wake, ko kuma a dasa bam ko wani abin fashewa da ka iya illata duk waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Hukumar ta yi wannan kira ne ranar Juma’a a wani yunƙuri na taya Musulmi murnar gabatowar watan azumin Ramadan da kuma lokacin azumin mabiya addinin Kirista.

Kakakin DSS, Peter Afunanya, ya gargadi malaman addini da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su guji yin amfani da mukamansu wurin tatsar tattalin arzikin al’umma, da kuma yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a lokacin waɗannan muhimman ayyukan ibada.

Afunanya ya ce, “Jama’a su yi taka-tsan-tsan kan hadurran da ke tattare da zama a wurin da ke da taron mutane da yawa, kuma a riƙa lura da masu ɗauke da abubuwan da suka yi kama da bom,

“Haka kuma, ana kira ga jama’a da su riƙa sanar da jami’an tsaro duk wata fargaba da suke fuskanta, da duk wani bakon abu, ko wani motsi da basu aminta da shi ba.”

A cewarsa, hukumar ta DSS ta san muhimmancin waɗannan ibadu da ake gudanarwa, shi ya sa ta ke bada shawarar ga masu yinsu, su ƙara fahimtar juna da tausayawa da mutunta juna a lokacin da ake gudanar da ibadun.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Tags