Muna fata a gano ’yan matan Chibok a zamanin Buhari – Zanna Mustapha

Mataimakin Gwamnan Jihar Borno Alhaji Zanna Umar Mustapha, ya ce suna fata za a gano ’yan matan Chiboka da mayakan Boko Haram suka saci shekara guda da ta gabata a lokacin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari da zai kama a watan gobe. Mataimakin Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a […]

Muna fata a gano ’yan matan Chibok a zamanin Buhari – Zanna Mustapha
Muna fata a gano ’yan matan Chibok a zamanin Buhari – Zanna Mustapha

Mataimakin Gwamnan Jihar Borno Alhaji Zanna Umar Mustapha, ya ce suna fata za a gano ’yan matan Chiboka da mayakan Boko Haram suka saci shekara guda da ta gabata a lokacin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari da zai kama a watan gobe.

Mataimakin Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Talatar da ta gabata, lokacin juyayin cika shekara daya da sace ’yan matan na Chibok.
Mataimakin Gwamnan wanda ya ce Shugaba Goodluck Jonathan mai barin gado bai yarda an sace ’yan matan ba, sai da aka dauki dogon lokaci, wanda hakan ya taimaka wajen bacewarsu ya ce, “Na tabbata in Allah Ya yarda wannan gwamnati ta Buhari za ta yi iya kokarinta wajen kawo karshen wannan ta’addanci a kasar nan, kuma ina da yakinin gano ’yan matan da kuma kawo karshen ayyukan ta’addancin.”
Ya ce gwamnatin Jihar Borno ta ware makudan kudi domin daukar nauyin karatun ’yan mata 54 da suka kubuta daga hannun Boko Haram, wadanda tuni aka tura su kasashen waje da nufin inganta karatunnasu, a yayin da wasu kungiyoyi ke ta fafutukar ganin gwamnati ta yi hobbasa don gano ’yan matan.
A ranar 14 ga watan Afrilun bara ne ’yan Boko Haram suka sace ’yan mata kusan 300 a Sakandaren Chibok, inda 54 suka kubuta daga baya.
Malam Shettima Haruna daya daga cikin iyayen ’yan matan, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa: “Wallahi tun daga lokacin da aka sace ’ya’yanmu har zuwa yanzu ba ma iya barcin kirki, ba mu da sukuni kullum muna tunanin ’ya’yanmu. Kullum muna zaune ne muna faman sharbar kuka babu cin abinci babu walwala, gaba daya kamar an yi mana mutuwa, ga shi ba mu da tabbacin ranar da yaran nan za su dawo. Ba mu sani ba ma ko suna raye ko suna mace.”