Muna fata za a yi adalci a shari’ar ‘yan Boko Haram

Salam, Edita. Da farko dai muna matukar farin ciki da zuwan ranar da aka fara gabatar da shari’a ga ‘ya’yan kungiyar nan da aka fi sani da suna Boko Haram wadanda tun da suka fara kaddamar da ayyukan su al’umma ta shiga uku. Tsoro a gida, tsoro a kasuwanni, tsoro a wuraren ibada duka, tsoro […]

Muna fata za a yi adalci a shari’ar ‘yan Boko Haram

Salam, Edita. Da farko dai muna matukar farin ciki da zuwan ranar da aka fara gabatar da shari’a ga ‘ya’yan kungiyar nan da aka fi sani da suna Boko Haram wadanda tun da suka fara kaddamar da ayyukan su al’umma ta shiga uku. Tsoro a gida, tsoro a kasuwanni, tsoro a wuraren ibada duka, tsoro a makarantu, tsoro a asibitoci da makabartu. Ashe duk mai fatar samun natsuwa zai bukaci samun irin wannan rana da kuma aiwatar da shari’a ga duk wanda aka kama, amma kuma duk da hakan muna fatan adalci ya rinjayi rashinsa.  Watau muna fata duk wanda ba a tabbatar ba to kotu ce mai ikon yin abin da ya dace, wanda kuma suke da hannu to a tuna cewa fa sun kashe mutane da dama, kuma sun jikkata wasu da dama, sannan sun lalata dukiyoyi kuma sun tarwatsa al’umma. Misalai da dama wadanda tarihi ba zai manta da su ba sun hada da kisan manyan mutane, inda a shekarar 2014 sun hallaka Sheikh Muhammad Auwal Albani Zariya, a shekara ta 2012 sun kai hari a Hedkwatar ‘yan sandan Najeriya, haka a shekara ta 2014 a Yobe sun kai wa ayarin mabiya shi’a hari, ga kuma hari a masallacin jumma’a na Kano a shekara ta 2014, duka su ake zargi kuma an hallaka Sheikh Muhammad Adam Almasri a Gombe, ga kuma  Jami’ar Maiduguri baya ga kai mata hari da aka yi, sun hallaka wani malamin jami’ar. Duk wadannan ta’addancin su ake zargi da aikata wa. Ashe yi masu shari’a mai adalci shi ne kawai abin da mu ’yan kasa muke da bukata. Allah Ya ba kasarmu Najeriya zaman lafiya da wadata.

 Sako daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. Gidan Ummarun Dallage masoyin gwamnatin Baba Buhari. 07066434519/08080140820