Muna fim a Legas don mu bunkasa harshen Hausa- Jarumi Autan-Anti
An haifi jarumi Abdullahi Ibrahim wanda ake yi wa lakabi da Auntan Anti a Agege da ke Legas, amma ya yi makaranta a Hadeja da ke Jihar Jigawa. Ya bayyana dalilin da ya sa ya shiga harkar fim da kuma kalubalen da yake fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance: Me ya sa ka shiga […]

An haifi jarumi Abdullahi Ibrahim wanda ake yi wa lakabi da Auntan Anti a Agege da ke Legas, amma ya yi makaranta a Hadeja da ke Jihar Jigawa. Ya bayyana dalilin da ya sa ya shiga harkar fim da kuma kalubalen da yake fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance:
Me ya sa ka shiga harkar fim?
Autan Anti: Na shiga harkar fim ne saboda sha’awar da nake da ita. Ni mutum ne mai mutukar sha’awar fina-finan Hausa. A halin yanzu mun yi fim guda daya mai suna ‘Son Maso Wani’ amma bai shiga kasuwa ba. Na fito a abokin jarumin fim din. Ibrahim Abdullahi ne ya shirya fim din. Lokacin da na shiga harkar fim sai na rika burin in zama jarumin da ya yi fice. Don ni a rayuwata ina so na zama kamar fitaccen jarumin fina-finan Indiya mai suna Sharu Khan.
Shin kuna da kungiya a nan jihar Legas?
Autan Anti: E muna da kungiya sunanta AYA Production ; muna da alaka da kungiyar ’yan fim ta Arewa. Suna ba mu goyon baya tare da karfafa mana gwiwa. Suna gaya mana cewa idan muka ci gaba za su hada gwiwa da mu wajen shirya fina-finai. Kuma sun tabbatar mana idan za su yi fim a Legas ba sai sun zo da jarumai ba, za su rika daukar mu muna yi musu duk abin da suke bukata. Domin muna da jarumai maza da mata masu hazaka da basira da kuma biyayya.
Me ye alakar ku da masana’antar fim ta Nollywood da kuma kungiyar masu shirya fina-finai ta Yarabawa?
Autan Anti: Gaskiya alakar mu da su ba ta yi kwari ba don yanzu muka fara amma muna sa ran idan muka yi kwari sosai za mu kulla alaka da su. Muna jin Yarabanci sosai saboda a nan aka haife mu. Muna da sha’awar shiga cikin fina-finan su amma ina so ni sai na yi kwari a fim din Hausa kafin na shiga na wani yare. Ka ga kamar Ali Nuhu, sai da ya yi kwari ya kafu a fim din Hausa sannan ya shiga fim din Nollywood da na Ghana da sauransu.
Wane kalubale kake fuskanta a harkar fim?
Autan Anti: Gaskiya ne kalubalen da nake fuskanta shi ne irin yadda jama’a suka yi wa harkar fim wani irin kallo. Amma ina so su sani cewa harkar fim ba hanyar banza ba ce, hanya ce ta fadakarwa da ilimantarwa. Misali fim din da muka yi na ‘Son Maso Wani’ ka ga yana fadakar da iyayen da suke yi wa ’ya’yansu auren dole. Saboda haka duk wanda zai rika zagin mu ba mu damu ba saboda sana’a muke yi don mu rufa wa kanmu asiri.
Me ya sa ka zabi yin fim a Legas a maimakon Arewacin Najeriya inda Hausawa suke da rinjaye?
Autan Anti: Mun tsaya a Legas ne saboda mu bunkasa harshen Hausa. Saboda a nan kafin ka ga kungiyar fim din Hausa yana da wuya. To shi ya sa ka ga mun tsaya a nan Legas muna ta fafatawa.