Muna fuskantantar kalubale a yaki da Tamowa – Ummi el-Rufa’i
Yaushe aka kafa wannan cibiya taki mai yaki tare da ilimantar da mutane a kan cutar Tamowa? A takaice an kafa wannan hukuma ne a watan Janairun bana kuma makasudin kafawar shi ne, domin ilmantar da jama’a a kan cutar Tamuwa, watau karancin abinci mai gina ciki. Muna kuma bukatar taimakonku manema labarai wajen ilmantar […]

Yaushe aka kafa wannan cibiya taki mai yaki tare da ilimantar da mutane a kan cutar Tamowa?
A takaice an kafa wannan hukuma ne a watan Janairun bana kuma makasudin kafawar shi ne, domin ilmantar da jama’a a kan cutar Tamuwa, watau karancin abinci mai gina ciki. Muna kuma bukatar taimakonku manema labarai wajen ilmantar da jama’a da su gane muhimmanci tare da illar karancin abinci mai gina jiki ga yara.
Wadanne nasarori aka samu tun daga lokacin da aka kafa wannan cibiya?
Alhamdu lillahi, mun samu cikin ikon Allah mun fara ne da ilimantar da jama’a abin da ake nufi da Tamowa ta kafafen watsa labarai, tare kuma da sanar da jama’a illolin cutar Tamowa ga yara kanana. Mun kuma fito ds tsare-tsare da muke yi, inda ake koya wa mata irin girki da za su yi na gargajiya domin ciyar da yaransu masu fama da ciwon Tamowa. Mun kuma zauna da kungiyoyi masu yawa da ke da sani da ilimi ta yadda za mu iya hada abincin gargajiya da zai taimaka mana wajen magance wannan ciwo.
Mun kuma kafa cibiyoyi a kananan hukumomi uku da muke bayar da wannan magani na ciwon Tamowaý. A yanzu haka muna kananan hukumomi uku Zariya da Makarfi da Igabi. Kuma in sha Allahu muna da burin kafa wadannan cibiyoyi a kananan hukumomi 23 da ke jihar nan baki daya. A kowace karamar hukuma, muna fatan a samu asibitoci biyar da za su taimaka mana wajen yaki da ciwon tamowa a jihar nan. Haka nan Hukumar Sufuri ta Jihar Kaduna (KSTA) tana taimaka mana da motocinta a wadannan kananan hukumomi, inda suke kai mata asibitocin da aka zaba kyauta. In kuma Allah Ya yarda za mu aiwatar da wannan tsari a sauran kananan hukumomi idan mun kafa wadannan cibiyoyi.
Wane kalubale kuke fuskanta a wannan aiki na yaki da cutar Tamowa da karancin abinci mai gina jiki ga yara?
Gaskiya kalubalen suna da yawa. Da farko dai ma’aikatan asibitin ma akwai bukatar kara ba su horon da ya dace a kan yadda za su tafiyar da batun tare da kuma yadda za su rika kulawa da yaran. Haka kuma mutane dole sai sun canza yadda suke tafiyar da rayuwarsu. Misali, za ka ga mace mai juna biyu babu wanda ya damu da irin abincin da take ci ko kuma ka ga babu wanda ya damu da ta rika zuwa awo a asibiti, da irin magungunan da za ta sha, wanda ta haka ne cutar ke farawa. Za ka ga kuma mutane na boye yara masu irin wannan cuta wai saboda kunya. Sannan a ki kai su inda ya kamata su samu kulawar da ta kamata.
Dole mu canza yadda muke cin abinci a gida, domin za ka ga abincin mai gina jiki da ya kamata a ce yaro ya ci sai a bai wa maigida. Misali, nama da sauran abinci mai gina jiki. Yaro karami shi ya fi bukatar nama isassashe ba mahaifi ba wanda ya rigaya ya girma. Matsalolin dai suna da yawa sai dai kawai a ci gaba da wayar da kan jama’a su rika yin abin da ya dace, domin a samu damar kawar da wannan cuta a jihar nan.