Muna goyon bayan Sanata Ningi — Gwamnan Bauchi

A ranar Talata aka dakatar da Sanata Ningi kan zargin da ya yi na cewa an yi cushen N3trn a Kasafin Kuɗin bana.

Muna goyon bayan Sanata Ningi — Gwamnan Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad ya nuna goyon bayansa ga Sanata Abdul Ahmed Ningi, dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya da aka dakatar.

A jiya Talata ce Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Ningi kan zargin da ya yi na cewa an yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a Kasafin Kuɗin bana, lamarin da ya sanya ya yi murabus daga mukaminsa na Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa (NSF).

Da yake jawabi yayin taron Majalisar Zartarwa jihar a Gidan Gwamnati da ke Bauchi, a ranar Larabar gwamnan ya ce yana tare da Ningi, a matsayin ‘yan adawa a majalisar dattawa.

A jawabin nasa na ranar Laraba, Gwamnan ya ce, “A matsayinmu na ‘yan adawar Gwamnatin Tarayya, za mu faɗi wasu abubuwan da ya kamata a yi a cikin ra’ayinmu na gaskiya, amma ba nufin mu ba ne mu wulakanta kasarmu.

“Jiya na yi baƙin ciki sosai. Majalisar Dattawa ta dakatar da ɗaya daga cikin fitattun ’ya’yanmu mu daga Bauchi saboda faɗin gaskiya, domin ya tashi tsaye ya zama fitilar gaskiya.

“Hakazalika ban san abin da za mu yi ba amma za mu tattauna a sirrance don ganin abin da za mu iya yi don tallafa masa domin ina goyon bayan duk abin da yake yi.

“Kuma wannan ita ce fuskar ‘yan adawa, musamman idan abin da yake faɗi gaskiya ne.

“Bai yi saurin zuwa kafafen yada labarai ba amma, tabbas, ya nuna jajircewa kuma dole ne mu kasance tare da shi.

Kazalika, ya ce gwamnati za ta raba wa al’umma a fadin jihar tallafi, domin rage ƙuncin rayuwa da ake fuskanta.

Ya buƙaci kwamishinoni da su koma kananan hukumominsu don tabbatar da cewa an raba kayan abincin yadda ya kamata.

“Dukkanku za ku koma karamar hukumar ku don tabbatar da cewa an raba kayan abinci daidai gwargwado.”