Muna goyon bayan sasantawa da ’yan Boko Haram – Gwamnatin Yobe

Gwamnatin Jihar Yobe ta nanata ba da cikakken goyon baya ga kwamitin Gwamnatin Tarayya don sasantawa da ’ya’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram domin samar da zaman lafiya musamman a jihohin Borno da Yobe da suka fi fuskantar matsalar.Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam ne ya […]

Muna goyon bayan sasantawa da ’yan Boko Haram – Gwamnatin Yobe
Muna goyon bayan sasantawa da ’yan Boko Haram – Gwamnatin Yobe

Gwamnatin Jihar Yobe ta nanata ba da cikakken goyon baya ga kwamitin Gwamnatin Tarayya don sasantawa da ’ya’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram domin samar da zaman lafiya musamman a jihohin Borno da Yobe da suka fi fuskantar matsalar.
Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam ne ya bayyana haka a yayin da yake tattaunawa da ’yan kwamitin a karkashin shugabansa Ministan Ayyuka na Musamman Alhaji Kabiru Tanimu a ziyarar da suka kai gidan gwamnatin jihar da ke garin Damaturu.
Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce muddin ana son a samo bakin zaren samar da zaman lafiya kan wannan rikita-rikita da ta dabaibaye yankin, dole ne a yi zaman sasantawa don kawo karshen lamarin, “Don haka wannan yunkuri da ’yan kwamitin ke y i abin yabawa ne tare da fatan kwalliya za ta biya kudin sabulu,” inji shi.
Gwamnan ya ce a kokarin da gwamnatin jihar ke y i na samar da tsaro mai inganci ta samar da motoci  sama da 200 ga jami’an tsaro don gudanar da sintirin tare da wasu kayayyakin da za su tallafa wa jami’an tsaron su  tafiyar da ayyukansu cikin nasara.
Tun farko shugaban kwamitin Alhaji Kabiru Tanimu ya ce sun je jihar ce domi ganawa da masu ruwa da tsaki a harkokin tsaron jihar don tattauna irin ci gaban da aka samu da yadda za a shawo tabarbarewar harkokin tsaro tare da sasantawa da masu tada kayar baya.
Shugaban ya nanata cewa Gwamnatin Tarayya ta damu matuka kan tabarbarewar tsaro a yankin don haka ne ma ta kafa kwamitin da zai samo bakin zaren kawo karshen wannan tada kayar baya musamman ta sasantawa da kuma yadda za a yi musu afuwa.
 Alhaji Kabiru Tanimu ya ce ya y i imani cewa duk abin da zaman lafiya bai kawo ba, to rashin zaman lafiya ba zai taba kawo shi ba, don haka akwai bukatar a hada hannu don samar da zaman lafiya ta yadda masu tada kayar bayar za su ajiye makamansu don zaman sasantawa.
 Ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar kan asarar rayuka da dukiya da aka samu sakamakon tashe-tashen hankalin da ta yi fama da shi a baya tare da yaba wa gwamnatin bisa ga matakan da take dauka don samar da zaman lafiya a jihar.