Muna iya samar da alkamar da ake bukata a kasar nan – Manoma
Da alama kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na ajiye Dalar Amurka miliyan 422.9 (kimanin Naira biliyan 129) daga noman alkama bai yi wa masu ruwa-da-tsaki a harkar dadi ba, amma kuma manoma a shirye suke muddin za a tabbatar da haka. A kokarin gwamnatin na dakile shigo da alkama da kashi 50 cikin 100, […]
Da alama kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na ajiye Dalar Amurka miliyan 422.9 (kimanin Naira biliyan 129) daga noman alkama bai yi wa masu ruwa-da-tsaki a harkar dadi ba, amma kuma manoma a shirye suke muddin za a tabbatar da haka.
A kokarin gwamnatin na dakile shigo da alkama da kashi 50 cikin 100, ta kara haraji da kashi 10 daga kashi 50. Amma hukumar kasuwanci ta Jihar Legas ta ce wannan mataki na gwamnati yana shafar harkar fulawa da maciya burodi kuma hakan zai iya shafar dangantakar da ake yi ta huldar kasuwanci da Shugaban Amurka Donald Trump.
Ko da yake kasar na samar da tan dubu 600 wanda hakan ko kusa bai kai yawan tan miliyan 4.7 da kasar ke bukata ba. Kasar na shigo da tan miliyan 4.4 a shekara kuma hakan na shafar kudin ajiyar gwamnati.
Shugaban kungiyar manoman alkama ta kasa Alhaji Salim Muhammed ya musanta zancen da ake yi cewa, kasar nan ba ta da karfin samar da adadin tan din alkama da take bukata.
Ya kuma kara da cewa, “Najeriya za ta iya samar da yawan alkama a kan hekta miliyan 1.2.” ya ce, kasar nan na da manoma da ke da sha’awar noman alkama kuma yawancinsu masu noman shinkafa ne.
Ya ce, a yanzu jama’a sun koma noma fiye da shekarun baya musamman saboda shirin ba da rance na Gwamnatin Tarayya ‘Anchor Borrowers’ Programme’.
“Yanzu babban matsalar noman alkama ita ce, rashin masu saya amma a yanzu kungiyar masu fulawa ta Najeria ta amince za ta rika saye tunda sun yi gwajinta sannan sun amince da ingancinta. Saboda haka babu wani dalilin bude kofa kan shigowa da kayayyakin kasashen waje cikin kasar nan.
“Abin da muke cewa, shi ne ba nufinmu gwamnati ta hana shigowa da alkama ba, amma karin haraji zai kara wa masu zuba jari kwarin gwiwar zuwa domin saka jari a noman alkama a kasar nan,” inji Alhaji Muhammad.
Abin da ya rage inji shi, shi ne a duba duk wasu hanyayoyi da suka dace ta yadda za a rika noma alkamar da za ta ishi masu bukatarta a kasar nan.
“Idan har aka tallafa wa masu noman alkama musamman a yankunan da ke da kasar noma mai kyau kamar yadda hukumomin bincikenmu suka nuna, ko shakka babu Najeriya za ta iya noman alkama mai yawan gaske wadda ka iya rage alkaman da ake shigowa da ita daga wasu kasashe.
“Idan har da gaske gwamnati take wajen rage abin da ake shigowa da shi dole sai ta tallafa wa masu noman alkama da iri mai kyau mai inganci. Kuma dole a koma yin amfani da injinan noman zamani, domin har yanzu muna amfani da dabarun noma don ci ne kawai.
“ Akwai bukatar mu tashi daga noma don ci kawai zuwa noma domin kasuwanci ko da kuwa ba don kasuwanci kadai za a yi ba. Dole mu dan rika surkawa da noman kasuwanci,” inji shi.
Alhaji Salim, ya ce kasuwanci kadan a sana’ar noma ba zai inganta ba sai an hada da noman kasuwancin zamani harkar za ta iya habaka.