‘Muna jira a yanke mana hannuwa shekaru uku bayan hukunci’

Wani dan rajin kare hakkin dan Adam a jihar sakkwato, Malam Kabir Dodo, ya himmantu wajen ceto wadansu matasa guda biyu da kotu ta bayar umarnin a yanke hannuwansu. Babbar  kotun shari’ar musulunci ta Sakkwato ce dai  ta yanke wa wadannan matasan hukunci bisa zargin satar kudi Naira dubu goma, inda Alkalin kotun ya ba […]

‘Muna jira a yanke mana hannuwa shekaru uku bayan hukunci’

Nasiru Direba ne a dama tare da abokinsa da aka rufe su tareWani dan rajin kare hakkin dan Adam a jihar sakkwato, Malam Kabir Dodo, ya himmantu wajen ceto wadansu matasa guda biyu da kotu ta bayar umarnin a yanke hannuwansu.
Babbar  kotun shari’ar musulunci ta Sakkwato ce dai  ta yanke wa wadannan matasan hukunci bisa zargin satar kudi Naira dubu goma, inda Alkalin kotun ya ba da umarnin a yanke hannuwan wadanda ake zargin bayan sun yi zaman jiran hukunci na shekaru uku.
daya daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin, Nasiru Abubakar, mai tuka motar haya, dan kimanin shekaru 25, wanda aka tsare tare da abokinsa bisa zarginsu da sace Naira dubu goma mallakar wani fasinja da ya shiga motarsa a shekaru uku da suka gabata, cewa ya yi, “Na yi imani da kaddara kuma dukkanin abin da ya faru da mu na dauka kaddara ce daga Allah. Ba mu son a yanke mana hannuwa, don tsarewar da aka yi mana a kan laifin da ba mu aikata ba, sam haka ba ta bisa ka’ida.”
Babbar kotun shari’ar musulunci ta biyu da ke Sakkwato, a karkashin jagorancin kadi dan Tsafe tun a shekarar 2010 ta ba da umarnin a yanke hannuwan dama na Nasiru Abubakar da Anas Muhammad, dukkaninsu direbobin motocin haya ne, bisa zarginsu da sace Naira dubu goma mallakar fasinjan da suka dauko a kan hanyar  zuwa Tambuwal daga karamar Hukumar Shagari.
Tun a shekarar 2010 wadanda aka yanke wa hukuncin suke tsare a gidan yari ba tare da an guntule hannuwan nasu ba, kuma ba su daukaka karar wannan hukuncin  ba, saboda ba su da masaniyar cewa suna iya daukaka karar wannan hukunci cikin kwanaki talatin tun daga sanda aka yanke musu hukuncin yanke hannun.
Da yake zantawa da Aminiya, Nasiru Abubakar ya bayyana cewa, a matsayinsa na direban motar haya ya saba daukar fasinjoji daga garin Shagari zuwa Tambuwal. Ya kara da cewa, fasinjoji biyar ne suka shiga motarsa a garin Shagari kan hanyarsu ta zuwa Tambuwal. ‘Na dauki fasinjoji biyar daga garin Shagari wadanda ke son zuwa Tambuwal , amma kafin mu kai can, sai wani tsoho ya fara kuwwa yana cewa an cire masa kudi Naira dubu goma daga cikin aljihunsa, a daidai wannan lokacin  kuwa mun cim ma wurin bincike na ‘yan sanda, sai ya sheda wa ‘yan sanda faruwar lamarin. Sabili da haka a nan take ‘yan sanda suka damke mu, tare da garzayawa da mu zuwa hedkwatar ‘yan sanda da ke Sakkwato, inda suka tsare mu na tsawon kwanaki goma sha takwas, daga bisani suka kai mu babbar kotun shari’ar musulunci, ita kuma kotun ta bayar da umarnin a tsare mu a gidan yari ba tare da wata sheda ko bayyanar mai kara a kotun ba.’’
A hakikanin gaskiya tun sa’adda nake tsare a gidan yari kimanin shekaru uku da suka shude ‘yan uwana ba su yi kowace irin hobbasa na karbar beli na ba, ko kuma tsoma baki domin daukaka kara a kan hukuncin wannan kotun ba. Ni maraya ne, kasancewar iyayena sun rasu.” Inji Nasiru.
An gano lamarin wadannan mutanen ne a lokacin da jami’in gudanarwa na jihar Sakkawato kan kare hakkin dan Adam, Alhaji Kabiru Dodo, ya ziyarci babban Gidan Yarin Sakkwato, kimanin makonni biyar da suka gabata, domin ya duba aikin ginin wani masallacin da ake yi a can.
Alhaji Kabiru Dodo ya sheda wa Aminiya cewa daya daga cikin jami’an kula da gidan yarin ne ya jawo hankalinsa game da wadannan matasan biyu da ake tsare da su, bayan yanke musu hukuncin yanke hannuwa.  “A lokacin da na shiga gidan yarin a watan da ya gabata domin duba aikin masallacin da ake ginawa domin amfanin bursunoni, sai daya daga cikin  jami’an kula da gidan yarin ya jawo hankalina dangane da matasan biyu da ke tsare har tsawon shekaru uku da suka shude bisa zargin sace kudi Naira dubu goma ba tare da an gabatar da wata kwakkwarar sheda a kansu ba.  A bisa jinkai ga dan Adam ne ya sa na tuntubi wani lauyan kare hakkin dan adam, Barista Abdulhamid Zubairu domin ya sanya baki ga lamarin tare da daukaka karar hukuncin da aka yanke musu, mai yiwuwa ko za su tsira daga yanke musu hannuwa.’’
Ya cigaba da cewa, ‘a gaskiyar lamari, mun fahimci cewa ana tsare da su ne ba bisa ka’ida ba, kuma ba tare da samun taimakon kowa ba daga kowane fanni. A kan haka ne muka soma hankoron ceto wadannan matasan daga yanke musu hannuwa bisa ga hukuncin da babbar kotun shari’ar musulunci ta yanke,” inji shi.
A bayanin da ya gabatar a kotun ‘yan kwanakin nan, lauyan da ke kare wadanda ake tuhumar ya sheda wa kotun cewa ana tsare da matasan biyu ne tsawon shekaru uku da suka shude, a saboda haka suka daukaka kara a bisa hukuncin farko, kamar yadda kundin tsarin mulki ya bayar da damar a daukaka kara.
 A bayaninsa, alkalin kotun daukaka kara ta shari’ar musulunci da ke Sakkwato, kadi Tambari ya amince da wannan bukatar, ya kuma dage shari’ar har zuwa ranar goma sha hudu ga watan Nuwanba domin cigaba da saurarenta. Amma da lokacin ya yi sai aka sake dage zaman ba  a kuma sanya wata ranar ba.
Da yake tsokaci a kan wannan lamari, Barista Abdulhamid Zubairu ya sheda wa Aminiya cewa, ya kuduri anniyar yin dukkanin abin da ya wajaba wajen ceto wadanda ake zargi daga yanke masu hannuwan.