Muna jiran tallafin iri daga gwamnatin Gombe – Manoman Masara
A kwanakin baya ne Kwamishinan Ma’aikatar Gona ta Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Magaji Gettado, ya bayyana cewa gwamnati za ta bai wa manoman masara na rani irin shuka mai inganci kyauta da kudinsa ya kai Naira miliyan 20. Aminiya ta tuntubi Shugaban Kungiyar Manoma Masara ta Jihar, Mista Elkanah B. Gurati, inda ya ce ba su […]
A kwanakin baya ne Kwamishinan Ma’aikatar Gona ta Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Magaji Gettado, ya bayyana cewa gwamnati za ta bai wa manoman masara na rani irin shuka mai inganci kyauta da kudinsa ya kai Naira miliyan 20.
Aminiya ta tuntubi Shugaban Kungiyar Manoma Masara ta Jihar, Mista Elkanah B. Gurati, inda ya ce ba su da labari amma idan aka ba su ba za su yi mamaki ba domin a gwamnatocin baya ba a ba su kyauta ba sai dai akan ba su ne su sayar wa manoma a farashi mai sauki.
Ya ce idan aka ba su irin kyauta zai taimaka musu wajen habaka noman tunda an ce irin mai inganci ne za su karba su jarraba su gani.
Ya ce a fahimtarsa, gwamnatin jihar tana da kyakkyawar niyya ga manoma, inda ya ce, idan gwamnati za ta taimaki manoma ba shakka za a samar wa kasa abinci a wadace.