Muna kai yaranmu Kudu ne domin ilimi – ’Yar gudun hijirar Boko Haram
Wata mata mai suna Naomi Hassan Gwoza, wadda ’yar asalin karamar Hukumar Gwoza da ke Jihar Borno ce, wacce ita da yaranta suka yo gudun hijira zuwa Jihar Edo, a sakamakon matsalar Boko Haram, ta ce a yanzu haka sun fara samun daidaiton alamurransu.“Lallai a yanzu mun fara samun kwanciyar hankali amma da yake har […]

Wata mata mai suna Naomi Hassan Gwoza, wadda ’yar asalin karamar Hukumar Gwoza da ke Jihar Borno ce, wacce ita da yaranta suka yo gudun hijira zuwa Jihar Edo, a sakamakon matsalar Boko Haram, ta ce a yanzu haka sun fara samun daidaiton alamurransu.
“Lallai a yanzu mun fara samun kwanciyar hankali amma da yake har yanzu ba a rabu da fargaba ba saboda haka tsoro ya hana da dama cikin mutanenmu wadanda ba a kashe su ba su dawo, su tare a muhallinsu saboda wannan yanayi da yankinmu ya fada a ciki na kungiyar Boko Haram.” Inji ta.
Ta ce a dalilin haka ne ya sanya shugabannin majami’arsu suka yanke shawarar hanyar da za su bi domin taimaka wa irin yaran Kiristoci ’yan gudun hijira, wadanda yakin Boko Haram din ya raba su da iyayensu, kimanin shekara biyu zuwa uku da suka gabata. Dalili ke nan suke koya masu ilimi kasancewar sun baro makarantunsu a can garuruwansu na asali.
Matar kuma ta ba da haske a kan dalilin kwaso irin wadannan yaran zuwa Kudu. “Dalilin da ya sa muke jigilar irin wadannan yara muke kawo su nan Jihar Edo shi ne, domin su samu su ci gaba da samun ilimin addinin Kirista da ilimin zamani. Muna kawo su ne mu mika wa wani Fasto a nan cikin garin Benin.” Inji Naomi, wadda ba ta ambaci sunan wannan Fasto ba da kuma anguwar da yake zaune a garin na Benin.
Ta ce wadannan yaran da dama daga cikinsu marayu ne. Ta kara da cewa, cikinsu akwai wadanda iyayensu ’yan Boko Haram suka karkashe su, wasu iyayen kuma sun yi gudun hijira, ba a san inda suke ba a halin yanzu amma wadanda ta kawo su a wannan karon su 23 ne maza da mata, ta ce da sanin iyayensu. “Domin ni ina daya daga cikin mutanen da shugabannin majami’armu suka amince mana mu kwaso irin wadannan yara mu kai wurin karatu a jihohin Kudu kamar Jihar Edo.” Inji ta.
Ta ce wannan shi ne karo na biyu da ta taba kawo yara karatu garin Benin. “Don haka wadannan yaran da ka gani tare da ni a nan, amanarsu aka ba ni, domin in kawo su kamar yadda na yi maka bayani tun da farko. Mun samu izini daga fastocin majami’armu ta Jihar Borno kuma suna kyautata mana sosai a kan wannan jigilar yaran da muke yi daga Borno zuwa nan Jihar Edo.”
Sai dai kuma a yayin da hakan ke faruwa, wato shugabannin majami’u na Jihar Borno suke kokarin tallafa wa yara ’yan gudun hijira da jigilarsu zuwa birane na kudancin kasar nan, shi kuwa Alhaji Abubakar Garba, dan kasuwa a garin Benin, kira ya yi ga su malaman addinin Musulunci da kuma sarakunan gargajiya Musulmi na arewa da cewa; lokaci ya yi da za su nuna irin tasu gudummuwar ga irin yara marayu ’yan gudu hijira Musulmai na jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.
Ya ce: “Ya kamata ku wadannan jagororin, ku tashi tsaye ku dubi irin halin da yara marayu suke a ciki da kuma irin makomarsu a nan gaba, idan har an ce sun kasance a cikin irin wannan rayuwar kunci. Domin kowa ya sani, talauci da jahilci za su iya haifar wa al’umma fitintinu daban-daban na rayuwa kamar yadda ake gani suke faruwa. Domin idan muka duba a yanzu haka, yaran suna fama da wahalar rayuwa ta bangaren abinci, kiwon lafiya, wurin kwana da rashin tsafta kuma babu batun koyar da su addini ko ilimin zamani.
“Watakila ganin hakan ya sa mabiya addinin Kirista suka yanke shawara, suke kwasar nasu zuwa suna kai su wasu garuruwa na nan kudu, domin ko ba komai za su samu abincin gina jiki da karuwa da yaran za su samu a bangaren da ya shafi addininsu. Don haka wannan shi ne dalilin da ya sa na yi wa wadannan malaman addinin Musulunci da sarakunan gargajiya kira a kan cewa su ma su yi wata hobasa, domin kawo karshen halin kunci da yaran suke a ciki.”