Muna kan bakarmu kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata — NLC

Ba mun tafi ba ne mu yi ciniki amma muna nan kan bakarmu har sai mun kammala tattaunawa.

Muna kan bakarmu kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata — NLC

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC Joe Ajaero, ya ce suna nan kan bakarsu ta neman N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata a Nijeriya.

Kwamared Ajaero ya faɗi hakan bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Aso Rock da ke Abuja.

A yayin da Gwamnatin Tarayya ta miƙa tayin N62,000, ƙungiyar ƙwadagon ta cije kan N250,000.

Sai dai Tinubu ya ce yana buƙatar lokaci kafin ya aika da ƙudirin neman ƙarin albashi mafi ƙanƙanta zuwa Majalisar Tarayya.

Shugaban na NLC ya ce tattaunawa suka yi da Tinubu amma ba sasanci ba kan batun ƙarin albashin.

“Mun amince mu koma mu yi nazari kafin makon gobe,” in Kwamared Ajaero.

Da aka tambaye shi game da matsayarsu kan N250,000 sai ya ce “ba mun tafi ba ne mu yi ciniki amma muna nan kan bakarmu har sai mun kammala tattaunawa.”

Sai dai Ƙaramar Ministan Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta ce an yi tattaunawa mai ma’ana tsakanin shugaban ƙasa da kuma shugabannin na ƙwadago.

Ta bayyana fatan za a daidaita nan ba da jimawa ba.