‘Muna karatun allo amma ba mu da almajirai masu bara  Kudu’

Duk da cewa al’ummar Musulmi mazauna Kudu maso Kudu, suna kokarin koyi da kuma koyar da addinin Musulunci, karatun allo wanda karatu ne mai dadadden tarihi da har yanzu ake ci gaba da yinsa a ko’ina a sassan kasar nan,  a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin sabunta makarantar allo da aka faro shi a […]

‘Muna karatun allo amma ba mu da almajirai masu bara  Kudu’

Duk da cewa al’ummar Musulmi mazauna Kudu maso Kudu, suna kokarin koyi da kuma koyar da addinin Musulunci, karatun allo wanda karatu ne mai dadadden tarihi da har yanzu ake ci gaba da yinsa a ko’ina a sassan kasar nan,  a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin sabunta makarantar allo da aka faro shi a zamanin gwamnatin da ta shude daga Jihar Sakkwato, makarantun da karatun har yanzu na fama da kalubale.

Wakilin Aminiya a Kuros Riba ya leka garin Nasarawa wanda gari ne na ’yan asalin Arewa da aka kafa shi tun zamanin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida, inda ya iske wata makarantar allo da sauran makarantun sun kankama ka’in-da- na’in suna koyarwa. A zantawar wakilinmu da Shugaban Makarantar Tahfizul Kur’an, Nasarawa, Malam Shitu Sa’idu Muhammad, ya ce a Kudu almajirsan makarantun allo ba su zuwa bara kamar yada ake yi a Arewa, sai dai ya ce su ma suna fama da kalubale iri-iri da suka hada da kin biyan kudin mako na Naira 50 kacal.

Malam Shitu Muhammad ya ce “Makarantar tana fuskantar kalubale da yawa sai dai in fadi wasu daga ciki. Kalubale na farko yanzu shi ne ba mu kammala aikin ginin makarantar ba, ka gan su ajujuwa ne guda uku akwai bukatar mu sanya musu silin, mu yi musu filasta, mu yi musu ciko sannan akwai bukatar mu yi kujerun zama na dalibai,  kuma mu nemo karin malamai,” inji shi.

Ya ce kalubale na biyu kuma “Gaskiya muna fuskantar kalubalen rashin kular iyayen yara, duk yawan daliban nan, wadanda suke biyo sawun ’ya’yansu ba su wuce mutum uku ba, su duba shin sun yi karatun, me suka karanta, suna zuwa makarantar ko ba sa zuwa? Ba su wuce mutum uku ba saura ko oho yanzu Naira 50 na gaya maka ake biya kowane mako, amma Naira 50 din nan sai rai ya baci ba a kawo  ta ba, amma babban abin mamaki sai ka ga mutum ya dauki Naira dubu 10 ya biya kudin makarantar boko na yaronsa,” inji shi.

Bayan jin ta bakin sMalam Shitu, wakilinmu ya zanta da Sarkin Nasarawa Alhaji Sani Baba, game da matakin da masarautarsa ke dauka kan iyayen yaran da ake samun korafi daga malaman makarantun allo da na Islamiyya da ke yankin kan irin kalubalen da makarantun ke fuskanta, sai ya ce “Gaskiya mu Musulmi musamman na masarautata ta Nasarawa ana kokari sosai game da karatun addini malamai ma suna himma sosai haka zalika daliban ma haka. Matsalolin da muke samu su ne na iyayen yara da wadansu ba su son biyan hakkin malamai da suke karantar da ’ya’yansu. Abin mamaki za ka ga mutum zai kai dansa makarantar boko ya je ya kashe kudi mai yawa amma idan ya zo makarantar allo sai ka ga yana ja baya da kyar zai ya cire Naira dubu daya-dubu biyu ya ba malamin da yake karantar da yaransa. A kan irin wannan na kirawo taron iyaye yara da ’yan majalisata muka zauna aka nada kwamiti wanda zai gano matsalolin da yadda za a gane bakin zaren,” inji Sarkin.

Ya kara da cewa “Muna jiran kwamitin ya mika mana rahoton abin da ya binciko ya kuma ya bayar da shawarwari, idan mun ga ta fuskar al’ummarmu ne za mu dauki nauyin biyan kudin malaman idan kuma mun ga ba haka ba, za mu tilasta wa iyayen yara su rika biya, ta hanyar kowane karshen wata, kowa ga abin da zai rika kawowa da za a hada ana ba malamai. Ina ganin idan rahoton kwamitin ya fito za mu san yadda za mu yi.  Mun ba kwamitin mako biyu ya mika mana rahotonsa don mu dauki mataki.” Akwai makarantun allo da na Islamiyya sama da bakwai a inda Musulmin suke da zama har ma akwai makarantar sakandare, a garin na Nasarawa.