Muna kashewa kuma mu sha jinin wadanda muka sace-Shugaban barayi

Shugaban gungun masu garkuwa da jama’a da fashi da makami wanda aka kama a Jihar Neja, ya yi ikirarin cewa suna kashe wadanda suka kasa biyan kudin fansa tare da shan jininsu.   Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda, CSP Jimoh Moshood ne ya bayyana wa manema labarai a ranar Talatar da ta gabata […]

Muna kashewa kuma mu sha jinin wadanda muka sace-Shugaban barayi

Shugaban gungun masu garkuwa da jama’a da fashi da makami wanda aka kama a Jihar Neja, ya yi ikirarin cewa suna kashe wadanda suka kasa biyan kudin fansa tare da shan jininsu.
 
Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda, CSP Jimoh Moshood ne ya bayyana wa manema labarai a ranar Talatar da ta gabata cewa rundunar ta kama gungun mutum 16 da ke garkuwa tare da fashi da makami a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a garin Sabon Wuse da ke cikin karamar hukumar Tafa a jihar Neja.
 
Ya ce shugaban gungun bata garin, Ibrahim Umar ya bayyana wa ’yan sanda cewa ya kashe mutum 10 yayin da suke aikata danyen aikinsu.