Muna kira ga su Kwankwaso da su dawo da sauri- Jam’iyyar PDP
Shugaban Kwamitin Amitattun Jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin y ace dawowar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar Jam’iyyar PDP abin murna ne. Sannan ya yi kira ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da Shugaban Majalisar Tarayya, Sanata Bukola Saraki da sauran wadanda suka bar jam’iyyar das u dawo jam’iyyar da sauri. […]

Shugaban Kwamitin Amitattun Jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin y ace dawowar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar Jam’iyyar PDP abin murna ne.
Sannan ya yi kira ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da Shugaban Majalisar Tarayya, Sanata Bukola Saraki da sauran wadanda suka bar jam’iyyar das u dawo jam’iyyar da sauri.
“Mun riga amince cewa dan takarar Shugaban Kasa ya fito daga Arewa. Don haka ina kira gare ku mu hada karfi da karfe wajen nemo dan takara day a fi dacewa. Wanda zai kwace mulki daga Jam’iyyar APC a zaben 2019. Zaben 2019 na PDP ne.
“Dawowar Atiku abin murna ne. Yadda ya nuna jajircewa wajen dawo wannan jam’iyyar abin a yaba ne.
“Muna kira ga Shugaban Majalisar Tarayya, Bukola Saraki da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sauran ‘yan majalisu da suka bar PDP das u dawo da sauri. Idan suka dawo za mu zaune tare mu tattauna a kan batun shugabanci. Da batun wanda zai zama Shugaban Najeriya,” in ji Sanata Jibrin.