Muna kokarin inganta ba da wutar lantarki a shiyyar Saminaka –Injiniya Umaru

Manajan Harkokin Kasuwanci na Kamfanin Wutar Lantarki na kasa [PHCN]  na shiyyar Saminaka a Jihar Kaduna, Injiniya Garba Umaru ya ce suna kokarin inganta ba da wutar lantarki a shiyyar, domin jama’ar shiyyar su ji dadin gudanar da harkokin kasuwancinsu. Injiniya Garba Umaru ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a […]

Muna kokarin inganta ba da wutar lantarki a shiyyar Saminaka –Injiniya Umaru
Muna kokarin inganta ba da wutar lantarki a shiyyar Saminaka –Injiniya Umaru

Manajan Harkokin Kasuwanci na Kamfanin Wutar Lantarki na kasa [PHCN]  na shiyyar Saminaka a Jihar Kaduna, Injiniya Garba Umaru ya ce suna kokarin inganta ba da wutar lantarki a shiyyar, domin jama’ar shiyyar su ji dadin gudanar da harkokin kasuwancinsu.
Injiniya Garba Umaru ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Saminaka, inda ya ce muna son mu ga wutar lantarki ta inganta a shiyyar Saminaka, saboda idan akwai wutar lantarki za a sami ci gaban arziki.
Injiniya Garba ya ce shugabannin kamfanin na kasa, sun yanke shawarar bude shiyyar ta Saminaka ce ganin ne yadda harkokin kasuwanci ke bunkasa a yankin tare da yawan jama’a. Ya ce wannan shiyya ta kunshi kananan hukumomin Lere da Kachiya da Zangon Kataf da Kauru.
Ya ce a lokacin da aka bude wannan shiyya a watan Mayun da ya gabata, sun tarar da matsalolin rashin isasshiyar wutar lantarki a yankin, inda suka yi ta kokarin ganin sun magance ta.
Manajan ya ce sun bude kananan ofisoshi a Hayin-Gada da Unguwar Bawa da Lere, domin inganta samar da wutar lantarkin. “Kuma da zarar wata matsala ta taso akwai ma’aikatanmu a ofisoshin za su je su yi gyara a kan lokaci, ba sai jama’a sun zo babban ofishinmu na Saminaka ba,” inji shi.
Injiniya Garba ya ce babbar matsalar da suke fuskanta a shiyyar ita ce ta rashin biyan kudin wuta daga masu amfani da ita. Ya ce “Abin da muke bukata shi ne da zarar an kawo wa mutum takardar biyan kudin wuta ya biya a kan lokaci. Ba sai an je an yanke masa wutar ba.”
Ya ce wata masalar kuma ita ce ta barayi da suke zuwa tarasfomomi suna sace wayoyi. Don haka ya yi kira ga al’ummar yankin su taimaka musu wajen kare kayayyakin lantarkin tare da biyan kudin wuta a kan lokaci.