Muna kokarin kawar da bata-gari a kungiyarmu – Sardaunan Garu

Mataimakin Shugaban kungiyar Masu Maganin Gargajiya na kasa Alhaji Shafi’u Salisu (Sardaunan Garu), ya shawarci masu maganin gargajiya su kula da dokokin kungiyar a yayin gudanar da harkokinsu na bayar da taimakon magani ga jama’a.Sardaunan Garu wanda ya bayar da shawarar a yayin da yake ganawa da wakilinmu a Keffi, ya kara da cewa, “dole […]

Muna kokarin kawar da bata-gari a kungiyarmu – Sardaunan Garu
Muna kokarin kawar da bata-gari a kungiyarmu – Sardaunan Garu

Mataimakin Shugaban kungiyar Masu Maganin Gargajiya na kasa Alhaji Shafi’u Salisu (Sardaunan Garu), ya shawarci masu maganin gargajiya su kula da dokokin kungiyar a yayin gudanar da harkokinsu na bayar da taimakon magani ga jama’a.
Sardaunan Garu wanda ya bayar da shawarar a yayin da yake ganawa da wakilinmu a Keffi, ya kara da cewa, “dole duk mai bayar da magani ya yi rajista da kungiyarmu ta kasa (National Union of Herbal Medical Practitioners of Nigeria) domin a yayin da ya yi hakan ne zai amince cewa zai bi ka’idojin kungiya sau da kafa ta hanyar gudanar da sana’arsa  bisa gaskiya da rikon amana, wato ba zai cuci mutane ba ta hanyar ba su maganin da ya san na karya ne, ko kuma ya mayar da harkar ta zama ta neman kudi ido rufe. Idan mai magani ya yi haka, idan ya fada hannun hukuma babu ruwanmu da shi.’’
Mataimakin shugaban sai ya yi kira ga ’ya’yan kungiyarsu da su kasance masu tausayi da adalci a zuciyarsu kuma ya kasance don taimakon al’umma suke yin sana’ar, idan har suka yi haka tabbas za su samu duk abin da suke so,’’ inji shi.
“Ina  gargadin masu ba da maganin gargajiya wadanda suke bata sunayen abokan sana’arsu ta wajen sayar da magani na wani da sunan maganin wani, ma’ana mutum ya dauki maganin Sardaunar Garu ya bare alamar da ke like a robar maganin sa’annan ya lika a nasa, ko kuma mutum ya sanya riga mai kala ko alamar rigunar masu tallar maganin wani  kuma yana sayar da wani maganin na daban, ko kuma mutun ya sayi magani sai ya je ya kara ruwa ko wani gari don maganin ya yi auki ya rika sayarwa, babu shakka idan mun cafke irin wadannan bata-garin tabbas ba za su ji dadi ba, don haka a kiyaye.’’
Su kuma masu sayan magungunan gargaji, Sardaunan Garo ya ce ya kamata su yi la’akari da irin maganin da za su saya kuma a wajen wa za su saya.