Muna maraba da El-Rufa’i a Jam’iyyar NNPP — Kwankwaso
Ni ba shugaba ba ne kawai na Kano, ni ne jagoran wannan jam’iyya a ƙasa baki ɗaya.
Jagoran Jam’iyyar NNPP na Ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ƙofar jam’iyyar a buɗe take ga duk wanda ke da ra’ayin shiga , ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i.
A baya-bayan nan dai an ga wani bidiyo da ke nuna wata ziyara da Sanata Kwankwaso ya kai wa tsohon Gwamnan na Kaduna a gidansa.
Malam Nasir El-Rufa’i dai ana zargin ya samu saɓani da Gwamnan Jihar da ya gaje shi, Sanata Uba Sani, abin da ya sa wasu ke ganin zai iya ficewa daga jam’iyyarsa ta APC.
Sanata Kwankwaso ya ce, har yanzu su ne halattattun ’ya’yan jam’iyyar kuma sun shige ta ce don samar da kyakkyawar manufa ta ceto Nijeriya da al’ummarta.
Sanata Rabi’u Kwankwaso yana mayar da martani ne kan iƙirarin korarsa daga Jam’iyyar NNPP da wasu ’ya’yan jam’iyyar suka ce sun yi, a kwanakin da suka gabata.
Sanata Kwankwaso ya ce babu wanda ke da ikon korarsa daga jam’iyyar da suka raya har ta kai ga matakin da ta kai a yanzu.
“Mu a ganinmu waɗannan mutane ba ’yan siyasa ba ne, ba su fahimci yadda tsarin yake ba.
“Ni ba shugaba ba ne kawai na Kano, ni ne jagoran wannan jam’iyya a ƙasa baki ɗaya, lallai ana so kowa ya shigo wannan jam’iyya, ba za a ce ba a son wani ya shigo ba, wannan jam’iyya ba ta kowa ba ce,’’ in ji Kwankwaso.
Ya ce, “Dimokuraɗiyya na da daɗi, kuma tana da wuya, a tsari duk lokacin da aka ce hukuma ko jam’iyya ta yi ƙarfi kamar yadda wannan jam’iyya take ƙanƙanuwa kafin mu shigo ta yi ƙarfi a yanzu, muna da sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai da Gwamna da Rabi’u Musa Kwankwaso da Buba Galadima da sauransu, to ka ga ai dole abubuwa su sauya daga yadda suke a baya.”
Ya ƙara da cewa saɓanin yadda wasu ke yaɗa jita-jita cewa sauyin tambari da jam’iyyar ta yi na da alaƙa da rikicin cikin gida da take fama da shi, Sanata Kwankwaso ya ce babu gaskiya a wannan lamari, domin sun ɗauki wannan mataki ne lura da yadda suka gamu da matsala wajen gane tambarin jam’iyyar a takardar ƙuri’a a zaɓen da ya gabata.
Sanata Kwankwaso ya ce “Sababbin launin da muka sauya da tutar jam’iyya, da shi kansa kundin tsarin mulkin jam’iyya abu ne da ya dace da wannan zamani, kuma ya nanata cewa samar da sabuwar alamar za ta ƙara haɗa kan ’ya’yan jam’iyyar tasu.
Tuni tsagin Jam’iyyar NNPP mai mubaya’a ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da korar ’yan Kwamitin Amintattun Jam’iyyar da suka dakatar da jagoran.
Jigon a jam’iyyar da ke biyayya ga Kwankwaso, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ne a wani taro da suka gudanar a Abuja a wani yunƙuri na sake fasalta al’amuran jam’iyyar.
Jam’iyyar dai ta rabu gida biyu, na Legas waɗanda su ne suka samar da jam’iyyar tun tana jaririya shekaru da dama da suka gabata, da kuma ɓangaren Abuja mai biyayya ga Kwankwaso, waɗanda suka raya jam’iyyar bayan shigarsu gabanin zaɓen 2023 da ya gabata.