Muna matukar bukatar jiragen sama mallakar Najeriya – Kyaftin Bala Jibir

Kyaftin Bala Jibrin kwararre ne kan harkokin tukin jirgin sama, kuma ya yi kwasa-kwasai da dama kan ilimin tukin jirgin sama a ciki da wajen Najeriya. Ya kuma yi aiki a Ma’aikatar Zirga Zirgan Jiragen Sama ta Tarayya, snanan ya rike mukamin Darakta a Ma’aikatar kafin ya yi ritaya, gogaggen dan siyasa ne da ya […]

Muna matukar bukatar jiragen sama mallakar Najeriya – Kyaftin Bala Jibir

Kyaftin Bala Jibrin kwararre ne kan harkokin tukin jirgin sama, kuma ya yi kwasa-kwasai da dama kan ilimin tukin jirgin sama a ciki da wajen Najeriya. Ya kuma yi aiki a Ma’aikatar Zirga Zirgan Jiragen Sama ta Tarayya, snanan ya rike mukamin Darakta a Ma’aikatar kafin ya yi ritaya, gogaggen dan siyasa ne da ya rike mukamai daban-daban cikin harkokin siyasa a kwanakin baya ya zanta da manema labarai  a Bauchi kan abin da ya shafi harkar zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya da ma bukatar da ’yan kasa ke da ita, domin a samun Jirgin Sama Mallakar Najeriya, wanda ke dauke da sunan Najeriya a jikinsa, ga kuma tsarabar da wakilinmu ya dauko mana.

 

Aminiya: Yaya ka ga kokarin shugaban kasa na farfado da Jiragen saman Najeriya?

Kyaftin Jibir: kokarin da shugaban kasa ke yi don dawo da martaba da kuma jiragen saman Najeriya abu ne mai kyau da ya dace. Wani abu ne da ya kamata a ce an dawo da shi tuntuni. Kuma da yake yanzu Allah ya sa muna da shugaban kasa mai kishin kasa ko da a lokacin yakin neman zabe ya nuna kyakykyawar aniyyarsa na samar da jirgin saman Najeriya. Watakila ko da an dawo da shi ba zai amsa sunan da Jirgin saman Najeriya na da yake dauke da shi ba. Domin sunan Jiragen Saman na da da ake ce wa (Nigeria Airways ) ya mutu, mai yiwuwa a sauya masa masa wani suna, saboda ba za ka sake tada mataccen abu ya rayu ba. Muna sa ran za a samu wani sabon abu saboda dalilai masu yawa. A gaskiya ko ka sake farfado da sunan jirgin saman irin na da da ya shude zai sake mutuwa da wuri.

Aminiya: Kan wane dalili?

Kyaftin Jibir: Saboda dukkan wadanda a da can suke bin kamfanin ba shi, amma suka hakura saboda mutuwar kamfanin da zarar sun ji ya sake dawowa za su bankado takardun shari’o’in da suke da su su koma kotuna. Saboda haka ya kamata idan aka sake dawo da kamfanin Jiragen saman Najeriya, zai fara ne da sabon suna kuma sabon littattafan gudanar da ayyukansa. Ka ga Kamfanin Jiragen Sama na (Swiss Air) lokacin da ya durkushe da gwamnatin kasar taso ta sake farfado da shi sai ta sanya masa wani suna mai kusan kama da  sunan da aka kira shi da farko, amma da bambanci gaskiya, na da suna kiransa (Swiss air), amma wanda suka sake sai suka kira shi da (Swiss) kawai ka ga bambancin wancan akwai (air) wannan kuwa babu. Don haka na Najeriya idan za a dawo da shi akwai sunaye da dama in an ga dama sai a dauki wanda ya fi. Misali ko mu kira namu da (Nigeria Airlines) ko mu ce (Nigerian Airlines ) ko mu kira shi (Wings Nigeria) ko (wings of Nigeria) duka dai wanda aka dauka zai amsa sunan Kamfanin jiragen sama na Najeriya. ’Yan Najeriya za su ga sunan kasarsu a jiki za su yi farin ciki da alfahari da shi.

Aminiya: Wane dalili ya sa kamfanin jiragen saman Najeriya ya mutu?

Kyaftin Jibir: A kwai dalilai da yawa da suka jawo mutuwar kamfanin jiragen sama na Najeriya. Na farko yin katsalandan daga gwamnati, gwamnati za ta tura wa kamfanin ya ba da tikiti, amma ba za a iya biyan kudin ba, kuma wannan ya shafi gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma hukumomin gwamnati da makamantansu; na biyu cin hanci da karbar rashawa shi ma ya taimaka, da kuma yanke shawarwarin da ba su kamata ba kan kamfanin daga gwamnati.  Sai a ba da umurnin da bai dace ba ga manajojin kamfanonin daga gwamnati, da kuma tsoma baki wajen yadda ake gudanar da kamfanonin, inda wadansu daga cikin manajojin lardi na kamfanin sun yi zaman kakagida a inda suke aiki sun zama sune masu gidan ba a iya taba su, sai ya zama koma wane ne shugaban kamfanin in yayi kokarin daga manajan da ke Landan ko Jamus ko Faransa ko wata kasa daga inda yake sai a buga masa waya a hanashi, don yana aiki ga wani shugaba a Legas ko a Abuja. Kuma a ka’idar aiki ko a kasuwanci ko a gwamnatance akwai wa’adin da ya kamata ma’aikaci ya zauna a waje, sai a yi masa sauyi, idan har aka daina wadannan to za aci riba a sabon kamfanin da za a kafa, kuma zai rayu ya samar da amfani mai yawa,

Aminiya: Mene ne muhimmancin dawo da wannan kamfani ?

Kyaftin Jibir: A gaskiya al’amarin nada matukar Muhimmanci kwarai da gaske muna bukatar Jirgin Saman Nijeriya Mallakar Najeriya, kuma muhimmancinsa ya fi yawa akan abin da wadanda ke sukar lamirin farfado da shi suke fadi. Ka ga na farko saboda yawan jiragen kasashen duniya da ke safara a Najeriya mu ba mu da namu a kowace shekara muna asarar sama da Dala Biliyan biyu da Miliyan 300 ke fita daga kasar nan zuwa kasashen ketare, wadansu ma suka ce kudin sun kai Dala Biliyan Uku da ake fitar wa a gajeren lissafi mu tsaya a tsaka tsaki, a kalla Dalar Amurka biliyan biyu da miliyan 500 ake fitarwa zuwa kasashen ketare kowace shekara daga Najeriya, ta hanyar mayar da kudin zuwa kasashen da ke da jiragen. Wannan kudi yana da matukar yawan da zai yi amfani ga kamfanin jiragen sama na Najeriya. Wannan kudi Dala biliyan biyu da miliyan 500 zai iya sayen Jiragen sama  guda goma kuma sababbi, ka ga kudin yana da yawa. Ka ga bai kamata mu bari a ci gaba da yin haka ba. Batun da za mu iya hada kanmu mu yi abin da ya fi kamacemu. Ka ga wani dalilin kuma a yanzu haka koka yarda ko kada ka yarda muna da direbobin jiragen sama ’yan Najeriya sama da 250 da suke zaune ba su da aikin yi. Mafi yawansu matasa ne maza da mata, kodayake akwai manya cikinsu, amma matasan sune suka fi yawa wadanda yanzu ne suka zo za su fara aikin tukin jiragen sama wadanda ake jin za su shafe fiye da shekaru 30 suna tukin jirgin sama, amma ba su da aikin yi. Muna da matuka jiragen sama da 150 zuwa 180 suna shawagi kan hanyoyin jiragen sama mallakarmu.

Idan muka samu kamfanin jiragen sama mallakar Najeriya zai zama dukkan wadannan matasa za su samu ayyukan yi. Kuma ka ga kamar yadda shugaban kasa yake fadi cikin Yakin neman zabensa cewa zai magance matsalar rashin ayyukan yi. Idan aka sake kafa kamfanin a kalla za a samu guraben ayyuka fiye da 5,000 mutane da yawa za su samu ayyukan yi a wajen. Don kuwa burinmu shi ne idan an kafa wannan kamfani ya zama zai fara da jirage da yawa, wadanda za mu iya kai mutane wurare da dama da za mu iya zuwa. Kuma ka ga wannan kamfani yakan sanya wa ’yan kasa alfahari da kwanciyar hankali. Don duk dan Najeriya ba ya jin dadi in ya je filayen jiragen sama na duniya zai ga sunayen kasashe da dama da jiragen samansu da sunan kasarsu, amma ba za ka ga na Naeriya ba, ko sanarwa ba za ka ji da sunan cewa wannan jirgin Najeriya ne ya sauka daga Fatakwal zuwa Abuja ba, amma inda za ka ji dadi , amma a ce muna ganin (Kenya Airlines) (Ghana Air craft), wata rana na taba ganin jirgin kasar Ghana a Baltimore da ke kasar Amurka sai na ji ban ji dadi ba ace Ghana nada Jirgi har yana zuwa Amurka amma mu Najeriya ba mu da shi abin ya yi mini ciwo,

Aminiya: A kwai masu ra’ayin yin hadaka tsakanin kamfanonin jiragen saman ’yan kasuwa da gwamnati. Ya  ka ga gani?

Kyaftin Jibir: Gaskiya ko an yi haka ba zai yi aiki ba. Ana yin wannan hadakar ne bisa abin da kamfanonin ’yan kasuwa suke so ba irin wanda zaa ce doka ce ta kafa ba. Ka ga kamfanonin jiragen saman da muke da su na ’yan kasuwa kowa na so a ce shi ya mallaki abinsa, kuma shi yake gudanar da kayansa yadda yaso. Yawancinmu ba za mu ji dadin yin amfani da irin wannan tsari ba. Abin da muke so shi ne gwamnati ta kafa sabon kamfanin jiragen sama na Najeriya muna da yarjejeniyar kasuwanci da kasashe da dama. Kuma irin yarjejeniyar da kasashe biyu ke sanya hannu akai na safarar jiragen sama tsakanin kamfanoni jiragensu ne za mu hau sararin samaniyarku za ku hau namu, za a tsara yadda jiragen za su rika tafiya cikin mako  da sauran ka’idojin da suka kamata kamar wuraren da jiragen zai je a kasar zai je wuri guda ne kawai ko kuma zai iya zuwa wurare da dama. Kamar wanda zai iya sauka a Legas da  Abujada Kano da Fatakwal da sauransu, dukkan wadannan suna daga cikin yarjeniyoyin da muka cimmawa, mun cimma sama da 70 ko da yake nasan sama da 20 suna aiki, amma muna da sama da 70 ne. Idan da Allah zai taimakemu mu samu jirage muma mu rika zuwa wurinsu, kamar yadda su ma suke zuwa wajenmu. Abin zai yi kyau kwarai da gaske idan ba mu je ba, ana biyanmu dan wani kudi na gazawarmu wajen zuwa dukkan kasashen da muke da wannan yarjejeniya. Wannan kudi da ake biya ana ajiyesu ne cikin wani asusu a Babban bankin Najeriya (CBN) ana kiransa Asususn yarjejeniya, wannan asusun ba a amfani da shi kamar yadda ya kamata. Idan da za mu rika zuwa wuraren da muka cimma yarjejeniya za mu je ba za a biya mu dan wannan kudi ba. Kuma an huta da batun cewa ba a amfani da kudin yadda ya kamata tunda ma ba za a samu asusun ajiyar ba.

Aminiya: A matsayinka na matukin jirgin sama ko hukumominmu sun iya huldar kasuwaci da abokan cinikayya yadda ya kamata?

Kyaftin Jibir: Gaskiya wannan magana hukumomin jiragen samanmu sun iya huldar kasuwanci da girmama abokan hulda kamar sauran hukumomin tattalin arziki ko da yake in aka kwatanta mu da kasashen Yammaci za a ga akwai bukatar mu kara himma. Zan ba ka misali Shugaban kamfanin jiragen sama na Delta a shekarar 1982, shugaban kamfanin jiragen sama na Delta da ake kira (Delta Airlines) ya shiga jirgi don kawai ya gwada ma’aikatan jirgin, ya ga ya ya za su yi, sai ta tambaye shi, inda zai zauna ta karbi tikitinsa ba ta damu da hawan kawara da ya yi ta yi mata ba, damuwarta ya samu wajen da zai zauna a cikin jirgi. Ita  fa ba ta san shi ba, amma ta yi hakuri inda a ce ta mayar masa da martani kasan abin da zai faru, ya ya kake ji idan ka yi tuntube wa ma’aikatan jirgi a Najeriya kasan mene ne zai faru. Ba zan ce ba mu yin hulda da kyau ba. Idan ka je sauran hukumomin kasuwanci kamar na Gidan waya ko gidan samar da wutar lantarki za ka ga duk halayennu iri daya ne, amma ya saba da irin halayen mutanen da ke aiki a hukumomi irin namu a kasahen Yammacin duniya.na kasashen duniya na yi maka hidima kamar Basarake ko ina kake kamar kai kadai suka damu da kai a otel ko a wani wurin kasuwanci.

Aminiya: Wata babbar matsala da ake fama da ita a Najeriya ita ce yawancin jiragen saman da muke da su a kasar nan tsofaffi ne? 

Kyaftin Jibir: Na tabbatar idan aka kafa sabon kamfanin jiragen sama na Najeriya gwamnati ba za ta sanya tsofaffin jiragen sama ba, gwamnati za ta samar da sababbin jiragen sama ne. Gwamnati za ta tattauna ne kai tsaye da kamfanonin da ke kera jiragen sama, kamar su Boeing na kasar Amurka, da kamfani kasar Faransa. Gwamnati za ta tattauna da su kuma za ta bayar da tabbacin ayyuka masu kyau, kodayake watakila a ce gwamnati ba ita ce za ta mallaki kamfanin baki daya ba, amma ya kamata a ce ita ce ke da mafi yawan jari a ciki. Idan za a karbi shawarata ni na fi so gwamnati ta mallaki kamfanin baki daya. Daga farko in ya so daga baya gwamnati tasayar da kashi 40 cikin 100 na jarin ga ’yan Najeriya, kashi 30 cikin 100 ga ’yan kasar waje da ke da sha’awar zuba jari gwamnati ta rike kashi 30 cikin 100 abubuwan sun yi nasara. Gwamnati na iya sake sayar da kashi goma cikin 100 ga ’yan Najeriya ita ta ci gaba da rike kashi 20 cikin 100. Yin haka zai sa gwamnati ba za ta rika katsalandan cikin harkokin kowane lokaci ba. Kuma ba za ta rika yin soko-soko ba. Ka ga wannan kashi 20 cikin 100 din zai sa gwamnati a duk inda take tasa himma, don tana da jari a ciki in kuma jirgin ya samu wulakanta a wani wuri, gwamnati na iya amfani da matsayinta a dawo masa da martabarsa. Yin haka zai sa a  kare jirgin daga duk wani cin mutunci ko cin zarafi.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno