Muna murnar sako tagwayen amaren Zamfara

Assalamu alaikum, Edita. Alhamdulillah, duk kan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, hakika komi ya yi farko yana da karshe. Jaridar AMINIYA, Ina taya ’yan’uwa  da iyalen tagwaye biyu da aka yi garkuwa dasu a jihar Zamfara, wato Hassana Da Hussaina, murnar dawowarsu gida daga hannun bata gari masu satar mutane domin neman kudin […]

Muna murnar sako tagwayen amaren Zamfara

Muna murnar sako tagwayen amaren Zamfara

Assalamu alaikum, Edita. Alhamdulillah, duk kan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, hakika komi ya yi farko yana da karshe. Jaridar AMINIYA, Ina taya ’yan’uwa  da iyalen tagwaye biyu da aka yi garkuwa dasu a jihar Zamfara, wato Hassana Da Hussaina, murnar dawowarsu gida daga hannun bata gari masu satar mutane domin neman kudin fansa Allah ya kiyaye faruwar na gaba amin. Ta hannu guda kuma muna yaba wa Kungiyar Muryar Talaka reshen jihar Zamfara ganin irin yadda ta yi ruwa ta yi tsaki don ganin wadannan tagwaye sun dawo gaban iyalensu, hakazalika suma wadan da suka bada tasu gudunmowar ta hanyar bada tallafi kamar su: Sanata Kabiru Marafa, dama sauran al’ummar da basu bukaci a ambaci sunan su ba,  duka muna addu’ar Allah ya saka musu da mafificin alheri, kuma daman kowa ya taimaki wani shima Allah zai taimake shi, sannan kuma a karshen wasikar muna yin amfani da wannan dama wajen  yin kira da gwamnati dama mahukunta da su samar da wata doka mai tsanani kamar daurin rai da rai kokuma hukuncin kisa kan duk wanda aka sameshi da aikata laifin yin garkuwa da mutane da nufin karbar kudin fansa, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu amin summa amin.

Daga Hussaini Abba Dambam jihar Bauchi Tarayyar Najeriya, 08020814173.

 

’Yan PDP a yi hattara da ’yan bangan jam’iyya

Assalam Edita, Allah wadai naka yalala ce rakumin dawa yaga na gari, shugabanni na neman takarar mukaman Najeriya a PDP sun zama ’yan bangan jam’iyya, su ne masu zuwa nema wa PDP yakin zabe. Daga Mai Kunan Kobo Jada Adamawa 07034542318

 

Kira ga Dan Majalisa Alhaji Audullahi Iliya

Assalam Editan wannan Jarida mai albarka don Allah ka mika kukanmu ga dan majalisarmu Alhaji Audullahi Iliya Yaryasa da ya taimakamana a gyara mana titinmu da ya tashi daka Dogan kawo zuwa ruwan tabo zuwa faska, zuwa Tudun wada. Gadarmu ta karye kimanan shekara 4 amma idan damina ta yi sai murasa yan da zamuyi bamu da kowa sai Allah. Daga Shu’aibu Danjimmai Ruwantabo Tudun Wada Kano 07037238878

 

Kira ga talakawan Najeriya

Assalam fatan alheri a gareku ma’aikatan Jaridar Aminiya, Edita taimaka mini ka bani dama, na yi kira ga ’yan uwana talakawan Najeriya, bisa tunkarowar zabe, yana da kyau mu natsu wajen zaben shugabanni da wakilai nagari, kada muce sai dan takara yana wata jam’iyya sannan yake tsarkakakke, ko wacce jam’iyya mutum yake muddin mun san ya cancanta, mu zabe shi kawai, mu kuma daina siyasar kudi, domin kuri’arka ’yan cinka ce. amma idan an baku ku karba, sai dai yana yana da kyau mu zabi cancanta, Allah ya bamu shugabanni da wakilai nagari amin. Daga Murtala Ahmed Abubakar Kwalli Gidan Doki Kano {07068295953}

 

Tsokaci akan mulkin jam’iyyar APC

Assalam Edita, ina son ka bani dama domin in yi tsokaci ga ’yan jam’iyyar APC mai mulki wanda hakika ’yan Najeriya su na cike da mamaki akan tsarin da jam iyyar APC take tafiya a kai duk da cewa a lokacin da jam iyyar APC ta karbi mulki daga jam iyyar PDP a lokacin ta yi alkawarin gyara abubuwa da dama da suka shafi talaka, musamman karin albashi da gwamnatin ta yi alkawarin yi wa ma’aikata amma abin mamaki sai gashi an wayi gari Gwamnatin Tarayya dana jahohi sun sanya kafa sun shure maganar karin albashi sun ce sun fasa karin albashin ba zasu iyaba shin wannan shine adalcin? Daga Hadi Tsohon Sarki Daura-08136433609-08164205067

 

Jinjina ga Gwamnan Sakkwato

Assalam Edita, ka isar min da sakona kan ayukkan da gwamnatin Sakkwato ke aiwatarwa na ci gaba, tabbas Matawalle Magajin Sardauna ne na yi imani duk mutunen kirki a Sakkwato Matawalle ya ke yi a birnin Sakkwato mukam mun bi, mun amince. Daga Musty Sakkwato 08034068363

 

Kira ga masu neman Ganduje da sharri

Salam fatan alheri a gareku ma’aikatan jaridar Aminiya mai farin jini, don Allah Edita ka taimaka mini ka bani dama na yi kira ga gwamnan jihar Kano tare da daukacin masoya Gwamna Ganduje, bisa faifan bidiyo da yake ta yawo kan zargin karbar cin hanci da ake zargin Gwamnan da yi,  irin wadannan sharrance sharrance da hada hotuna na batanci da ake yi wa mutane masu mutunci ba yau aka saba ba, an yiwa tsohon Gwamna Shekarau, an yiwa mutane da dama masu daraja, saboda haka mu masoya Ganduje muna tare da kai dari bisa dari, da yardar Allah sai kun maimaita kai da Baba Buhari. Da yardar Allah mai neman Gwamna Ganduje da sharri sai ya koma kansa, Allah kuma ya shiga tsakanin nagari da mugu amin. Daga Murtala Ahmed Abubakar Kwalli Gidan Doki Kano 07068295953

 

Kira ga Aminu Bello Masari

Assalam Editan Aminiya mai farin jini ga kowa. A taimaka mani in yabi wanda ya biya mani kudin makarantar sakandire wato Barista Ibrahim Shehu Shema. Gwamnatin da ta gabata ta jihar Katsina ta daukewa kowa kudin makarantar sakandire [WAEC NECO] kyauta ne amma wannan gwamnatin biya ake yi ina kira ga Aminu Bello Masari ya biya kudin makaranta don Allah don Annabi. Daga Samiru Wada Kanyar-Ubandaba 08103585062

 

Kira ga Gwamnan Kano

Salam Aminiya, a mikamin sakona ga Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje 4+4 yakawowa kasuwar gwari ta kwanar Dangora dauki babbar kasuwa ce a Arewacin Najeriya babu kamarta tunda kasashen waje sun fi goma masu zuwa sayen kaya daga Legas suke saya yanzu sun dawo kwanar Dangora suke sayan kayansu. A taimaga Gwamna. Sako 08125555569

 

Martani ga Gwamnan Jihar Sakkwato

Jinjina ga jaridar Aminiya, ina so wannan jarida mai alfarma ta bani dama don na yiwa Gwamnan jihar Sakkwato martani, ya kai Gwamna ka nuna mana cewa jiharku cike take da badakaloli, sannan ba kishin al’ummarku ku ke yi ba saboda kuna boye hakikanin gaskiya saboda san kanku, to yanzu da kake cewa zaka tona asirin magabacinka wai domin magabatanku sunce kaja layi, amma yanzu tunda yana matsa maka shi zaisa ka tona barnarsa toh gaskiya ka tafka babban kuskure, tun duniya kenan inda kake da maboya, yo lahira fa? kana da maboya? shawara ka yi wa jiharka aiki da adalci kodan kwanciyar kabari. 08022672006

 

Sakon godiya Sakkwatawa

Assalam tabbas Sakkwatawa sun nuna halin dattako wajan fitowa kwansu da kwarkwata domin tarban Gwamna Tambuwal tabbas Sokoto ta Tambuwal ce yanzu mun gano ’yan bangar siyasa masu cewa su ake yi ba jam’iyyaba ashe ba suda kowa sai karya banza Sakkwatawa shaida ne akan haka gaba gaba Matawallen Daular Usmaniya Sokoto PDP muke yi. Daga Musty Sokoto 08034068363

 

Najeriya ta daga tuta a Nahiyar Afirka saura talakawa

Salam Aminiya! Najeriya ta daga tuta a Nahiyar Afirka ta kuma burge manya kasashen duniya musamman wadanda suke da sha’awar huldar ganin cinikayya ta kullu a tsakanin su, ganin yadda asusun ajiya na kasashen waje na Najeriya yake tumbatsa har ta kai ga yana jan hankalin wasu kasashe, a inda ta kai asusu ajiya ya kai tiriliyon 47 to wane hali talakan Najeriya ke ciki? wane kallo wadannan manyan kasashe suke wa talakawan Najeriya da shugabanninsu. hattara dai! Daga Basiru Danbazazzagi 08130616265

 

’Yan Najeriya mu zabi ’yan takara nagari

Salam Edit, don Allah ina so ka bani dama in danyi tsokaci akan zabe naga ba mai zuwa. Ko shakka babu akwai babban kalubale ga ’yan Najeriya, gashi dai man ’yan jam’iyyun nan guda biyu ne duk ’yan takarar ’yan Arewa ne, lalle shawara ta rage ga mai shiga rijiya, ma’ana zaben nagari, haziki, sadauki wanda zai tausaya wa talakka. Ya ’yan uwana ’yan Najeriya kar da mu yi wa kanmu zaben tumun dare, karda mu dawo muna nadama, mu tsaya muzabar wa kanmu wanda ba zamu yi nadama da nasani ba. Allah ya sa ayi zaben 2019 lafiya a gama lafiya. Daga Muhammad Kabir Salisu Gazarawa, mamba Muryar Talakka jihar Katsina, 08034200141

 

Jinjina ga Gwamnan Bauchi

Assalamu alaikum Editan Aminiya, Allah ya tsunduma ku a aljannatul fidausi, ku mika mun godiya ta ga Gwamnan jihar Bauchi M.A. Abubakar bisa kokarin hada kan ’yan siyasan jihar Bauchi don a ciyar da jihar mu gaba. Daga Babawo Chelsea Kofaran Me Wikki Tourists Da Elkanemin Warriors A Unguwan Rafin Albasa A Birnin Bauchi 08058323531

 

Kira ga shugaban Najeriya a kan Gwamnoni

Assalamu alaikum Editan Jaridar Aminiya, mai albarka don Allah ku bamu dama mu yi kira ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari da shugabanin jam’iyyar APC na kasa da ya kamata su rage ikon gwamnonin jahohi akan gudanar da aikin jam’iyya muddun suna so jam’iyyar APC ta kai bantan ta a jihohi, domin wasu gwamnoni suna kama karya a jahohin su, gyara kayan ka dai bazai zama sauke mu raba ba.” Daga Aminu Adamu Malam Madori, da Rabiu Dakot Dunari Malam Madori A Jihar Jigawa,08182315298.

 

Kan batun karin albashi

Fatan alheri ga gidan jaridar AMINIYA a yau ina so ne ku bani dama na tofa albarkacin bakina, kan batun karin albashi da kungiyoyin ma’aikata suke bukata a gurin Gwamnatin tarayyar Najeriya, toh ni dai ana wa ra’ayin bana goyon bayan karin albashin ko kadan, saboda dalilai kamar haka, na farko dai abin da yafi muhimmanci shi ne amai makon wannan karin albashi gwamma ace Gwamnati ta kara yawan ma’aikata, sannan abu na biyu kuma masana suna hasashen cewa, karin albashin zai kawo hau hawar kayan masarufi kunga kenan an yi aikin baban giwa, sannan kuma gashi muna da dubban matasa da suka kammala karatu babu abin yi, shin me yasa kungiyoyin ma’aikatan basa fafutukar ganin an dauki matasa aiki? sai dai kullum muji suna neman karin albashi? An ya kuwa ba su na yi ba ne saboda kashin kansu ? ya Allah kajikan talakan Najeriya ba don ya mutu ba. Daga Idriss M Idriss Damaturu Jihar Yobe 08033775767