…Muna neman amintattu da suka iya mulki ne – Sakataren Gwamnatin Kebbi
Tun hawan Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu mulki ba da dadewa ba, ’yan adawa suka fara surutai cewa ya kamata ya nada kwamishinoni. Bayan abokan adawa, yanzu haka ta kai hatta wadanda suke jam’iyya daya da Gwamnan sun fara korafi saboda rashin nada kwamishinoni da masu taimaka masa a wannan tsawon lokaci. Yanzu […]

Tun hawan Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu mulki ba da dadewa ba, ’yan adawa suka fara surutai cewa ya kamata ya nada kwamishinoni.
Bayan abokan adawa, yanzu haka ta kai hatta wadanda suke jam’iyya daya da Gwamnan sun fara korafi saboda rashin nada kwamishinoni da masu taimaka masa a wannan tsawon lokaci. Yanzu dai in ban da Sakataren Gwamnatin Jihar da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, babu wani mutum da Gwamna Bagudu ya nada.
Wakilinmu ya tuntubi Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Alhaji Babale Umar Yawuri, ko mene ne dalilin rashin nada kwamishinoni, ga shi har an shiga wata na shida Gwamna na kan mulki?
Sai ya ce, akwai abubuwa da dama da za a yi la’akari da su kafin a ba mutum mukami da suka hada da irin amincin da yake da shi kan dukiyar jama’a da iya tafiyar da mulki da sauransu. Ya ce, kafin a ba mutum mukami sai ka duba mukaman da ya rike a baya da kuma yadda ya tafiyar da ayyukansa.
Daga abin da Gwamna ya gani tunda ya kama ragamar mulkin Jihar Kebbi, yana bukatar mutanen jihar masu kishinta da za su yi aiki wurjanjan, masu ilimi da gogewa da sadaukar da kai, ba masu ci amana ba. Ya ce kowa ya yi don kansa da Ubangijinsa don amfaninsu. “Abin takaici muna da mutane masu ilimi da kwarewa a Jihar Kebbi amma kowa kansa ya sani- nawa zai samu cikin kankanen lokaci,” inji shi.
Sakataren Gwamnatin ya kara da cewa, Gwamna Abubakar Atiku zai duba ’yan siyasa da kwararru, kuma hakika zai zakulo masu mutunci ya dora musu nauyin kula da ma’aikatu da hukumomin gwamnati. Ya ce, matukar ana bukatar cimma alkwuran da aka yi wa al’umma, wajibi ne a yi kyakkyawar nazari dangane da yanayin kudin da ake kashewa da yanayin yadda ake gudanar da harkokin gwamnati na yau da kullum.
Ya ce, “Amma duk da haka kusan komai ya kammala kuma cikin yardar Allah daga yanzu zuwa wani lokaci za mu aika da sunayen kwamishinonin zuwa majalisa, ita kanta majalisar a nata bangare ta bayyana shirin da take yi don tantance sunayen da Gwamna zai gabatar mata.”
Majiya mai tushe ta labarta wa wakilinmu cewa majalisar dokokin jiha ta kara himma don yi wa amintattun na Gwamna hisabi da binciken halayensu yadda ya dace don gudun kada a yi saka da mugun zare. “Ina tabbatar maka cewa majalisa a shirye take ta tantance sunayen da za a gabatar mata koda kuwa suna cikin hutu ne, za su dawo domin yin zama na musamman a kan sababbin kwamishinonin,” inji majiyar.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto jama’a sun kashe kunne don jin sabon labari daga fadar gwamnatin jihar kan wannan lamari.
Wakilinmu ya tambayi wani lauya mai zaman kansa a jihar, Aminu Kalgo, ko doka ta nuna lokacin nada kwmishinoni, sai lauyan ya ce, kai tsaye sashe na 192 ya yi bayanin cewa babu inda aka kayyade wa Gwamna cewa ga lokacin da ya wajaba ya nada kwamishinoni, amma ya nuna Gwamna ya yi kwamishinoni, amma bai kayyade lokaci ba, sai a dubi manufarsu domin a nada su.
Ya ce idan aka mika wa majalisa sunayen an ba ta ikon ta tantance su a cikin kwana 21, idan har aka kai wadannan kwanaki ba ta yi magana ba, iyaka za a dauka wadannan mutane sun zama kwamishinoni, kuma Gwamna zai nada su ne gwargwadon yawan da ya ga dama.
Wakilinmu ya tuntubi Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PDP a jihar Alhaji Umar Abdullahi kan rashin nada kwamishinnonin, inda ya ce bai kamata gwamnati ta dauki dogon lokaci ba tare da kwamishinoni ba, ya ce wannan zai iya kawo tarnaki ga tafiyar gwamnatin, domin idan gwamnatin ba ta da Majalisar Zartawa babu wani ci gaba da al’ummar jihar za su samu komai na gwamnati tsaye yake cik.
Ya ce tun lokacin da suke kiraye-kiraye ga Gwamna Bagudu ya hanzarta kafa Majalisar Zartawar domin harkokin gwamnati su tafi daidai, ana ganin maganganu ne na’yan adawa, amma yanzu ga shi an yi taro na masu ruwa a tsaki na ’yan asalin jihar a ranar Litinin din makon jiya, inda tsohon Gwamnan Jihar Sanata Mohammed Adamu Aliero dan jam’iyyarsu ta APC,a cikin jawabinsa ya yi ga kira Gwamna Atiku Bagudu ya hanzarta nada Majalisar Zartawa domin gwamnati ta kafu da gindinta a ci gaba da yi wa jama’a aiki kamar yadda aka yi musu alkawari a lokacin yakin neman zabe.
Ya kara bukatar Gwamnan ya yi kokari ya yi zaben kananan hukumomi da yake ya yi mulki ya san illar da rashin haka a jiha da rashin ci gaban da yake kawowa ga al’umma.