Muna neman DSS ta sako Nwogwugwu nan take – PDP

Jam’iyyar PDP na kira ga hukumar tsaro ta DSS da ta sako kakakinta na jihar Imo Ambrose Nwogwugwu ba tare da wani sharadi ba. PDP na zargin jami’an DSS da tsare Mista Nwogwugwu bisa umurnin Gwamna Hope Uzodinma na jima’iyyar APC. Kakakin PDP na kasa Kola Ologbondiyan ya soki danniya da tozarcin da ya ce […]

Muna neman DSS ta sako Nwogwugwu nan take – PDP

Kola Ologbondiya, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa

Jam’iyyar PDP na kira ga hukumar tsaro ta DSS da ta sako kakakinta na jihar Imo Ambrose Nwogwugwu ba tare da wani sharadi ba.

PDP na zargin jami’an DSS da tsare Mista Nwogwugwu bisa umurnin Gwamna Hope Uzodinma na jima’iyyar APC.

Kakakin PDP na kasa Kola Ologbondiyan ya soki danniya da tozarcin da ya ce ake wa ‘yan adawa a Imo.

Ya zargi gwamna Uzodinma da fatali da tsarin demokradiyya da yunkurin muttsuke ‘yan adawa a jiharsa.

“Jam’iyyar PDP na yin tir da yadda ake amfani da karfin gwamnati ana zaluntar ‘ya’yanta saboba ra’ayinsu ko yin taruka yadda doka ta ba su ‘yanci.

“Tun da Uzodinma ya hau mulki yake bin hanyoyi iri-iri domin murkushe masu bambancin ra’ayi da nashi.

“PDP na Allah-wadai da wulakancin da aka wa shugabanta na Nguru Nweke, Mista Chidi Ihedioha wanda ‘yan sanda suka kulle.

“Ana zargin an kulle shi ne da umurnin wani dan Majalisar Wakilai na APC, saboda ya kira halastaccen taron jam’iyyarmu,” a cewar Ologbondiyan.