Muna neman mafita rikici a wurin Allah
Sannu a hankali gwagwarmaya da rikice-rikicen `yan kungiyar Jama`atu Ahlis Sunna Lid Da`await Wal jihad, da aka fi sa ni da Boko Haram, wadda asalinta daga Maiduguri, babban birnin jihar Barno tun a cikin watan Yulin 2009, bayan da `yan sanda suka kashe Malam Mahammadu Yusuf shugaban kungiyar na kasa baki daya, alhali sojoji da […]
Sannu a hankali gwagwarmaya da rikice-rikicen `yan kungiyar Jama`atu Ahlis Sunna Lid Da`await Wal jihad, da aka fi sa ni da Boko Haram, wadda asalinta daga Maiduguri, babban birnin jihar Barno tun a cikin watan Yulin 2009, bayan da `yan sanda suka kashe Malam Mahammadu Yusuf shugaban kungiyar na kasa baki daya, alhali sojoji da suka kama shi a farkon tashin tarzomar, sun tabbatar da cewa sun kama shi da ransa, suka kuma mika shi ga `yan sanda cikin koshin lafiyarsa, amma daga bisani `yan sandan suka ce ya mutu. Kullum sai kara rikicewa take, ta yadda ka iya cewa mahukuntan da alhakin samar da cikakken tsaron rayuka da dukuyoyin al`ummar kasar nan sun rude, sun mayar da annobar tamfar wani batu na siyasa, tsakaninsu da `yan adawa.
Tun a ranar 14-06-2011, kusan shekara biyu da barkewarsa kungiyar ta fara nuna ba fa da wasa take ba, a lokacin da ta fara kai harin kunar Bakin wake na farko a kasar nan a Hedkwatar `yan sanda da ke Abuja, jim kadan bayan da Sufeto Janar na sandan na wancan lokacin, Alhaji Hafiz Ringim ya kai ziyara Maiduguri, inda ya yi barazana irin ta masu mulki cewa za su murkushe `yan kungiyar cikin karamin lokaci. Bayan wata biyu da hari, wato ranar 26-80-11 `yan kungiyar sun sake kai wani harin makamancinsa a Ofis Majalisar dinkin duniya da ke Abuja, harin da ya kara rikita lissafin duk wani mai lissafi, bisa ga irin tsauraran matakan tsaron da ofishin yake da shi.
Zai yi wahala rana ta fito ta koma hannun Ubangijinta, ba tare da ka ji an ce an kai hari nan ko can; ba dare, ba rana, a birane da karkara farmakin da matakan yaki ne iri-iri, inda sukan kasance munana a duk inda aka kai su. Gwamnatin ta kafa Kwamitin Ministan ayyukan na musamman, Alhaji Tanimu Turaki da ta dora wa alhakin tattaunawa da `yan kungiyar ta Boko Haram da sauran jama`ar kasa don gano bakin zaren. Kwamitin da ya bada rahotansa a bara, amma har yau ba sakamakon rahoton, bare matsayin gwamnatin tarayyar.
Ana cikin irin wannan hali na fargaba a jihohi irinsu Barno da Yobe da Adamawa, inda rikicin ya fi ta`azzara har gwamnatin tarayya ta sanya masu dokar tabaci a wadannan jihohi uku tun bara. Can kuma sai ga bullar hare-hare da sace-sacen shanu da rigingimun Fulani Makiya da Manoma a jihohi irinsu Filato da Katsina da Zamfara da Kaduna da Nassarawa da Binuwai, sai kuma ga rikicin jihar Taraba mai kama da na kabilanci da addini a Wukari, rikicin da kusan kwanaki bakwai an kiyasta an rasa rayuka kusan100. Kwatsam kuma sai ga harin kunar bakin wake da aka kai a cikin tashar mota ta Nyanya da ke kusa da Abuja da safiyar Litinin 14-04-14, inda aka kashe mutane 75, aka kuma jikkata sama da mutane 120.
kasa da awa 24, sai kuma ga batun sace `yan matan a Sakandaren gwamanati ta Chibok a jihar Barno, har 273, wadanda aka kiyasta zuwa ranar Lahadin da ta gabata kimanin `yan mata 39, kawai suka samu kubutowa. Sai kuma ga harin garin Yana da ke cikin karamar hukumar Shira ta jihar Bauchi, wanda aka kai a Makarantar Sakandare ta `yan mata da gidajen Malam dana mutanen gari da Bankin gari, amma dai Alhamdulillah, in ban da wani karamin yaro da ya rasa ransa, babu asarar da aka yi. Wannan rashin zaman lafiya haka ake fama da shi a dukkan sassan kasar nan, ta`addanci irin na `yan fashi da makami da ya game kasa, a yankin Neja-Delta ana fama da musifar sace mutane da ta`addanci fasa bututun da satar man fetur din. Mace-mace kuwa sai dai Allah Ka yi mana magani.
Dadin dadawa kafin wannan lokaci, abokan zamanmu musamman Kiristoci sun ta zargin cewa musulmai ne suke yakarsu, da aniyar su shafe, ko su tilasta masu shiga addinin musulunci. Alhamdulillah! yanzu lokaci ya sanya kungiyar Kiristocin kasar nan, wato CAN, ta fahimci cewa akasarin wadanda ake kashewa musulmi ne, kuma ko kusa ba batun yunkurin sai an musuluntar da su.
Abin da nike son yin magana a yau bai wuce irin yadda gwamnatin tarayya da jam`iyyar PDP, mai mulki da gwamnatin tsakiya suka mayar da wannan mummunan hali na tabarbarewar yanayin tsaron kasar nan wani batu na siyasa ba. Alal misali an shiga cacar baka tsakanin shugaban kasa da gwamnan jihar Adamawa Alhaji Murtala Nyako, a lokacin da gwamnan ya zargi gwamnatin tarayya da iza wutar rikicin. Sai gwamnatin ta mayar da martini cikin fushi ta hannun mataimaki na musamman ga shugban kasa.
Shi kuwa Sakataren yada labarai na jam`iyyar PDP na kasa baki daya Mista Metuh Olisa, shi kuma, ya zargi Janar Muhammadu Buhari, jigo a cikin jam`iiyar adawa ta APC da cewa dan kungiyar Boko Haram ne, bisa ga wai maganar da Janar Buharin ya taba yi a shekarar 2011, inda ya ce za su hana zaman lafiya a kasar nan, muddin wai bai ci zabe ba. Tuni Janar din ya mayar da martini cikin fushi, inda ya tura wata wasika ga jam`iyyar PDP, kan lallai ta nemi gafararsa a bainar jama`a cikin mako guda, abin da rashin yin hakan zai sanya alkali kadai zai raba su.
A can jihohin Barno da Yobe da Adamawa, mahukunta da dattijan jihohin na cacar baki tsakaninsu da shugaban kasa, akan babu bukatar ya ci gaba da kakaba musu dokar ta baci, bisa la`akari da cewa shekara daya da aka sa musu zuwa yanzu ba ta tsinana komai ba.
A takaice, wasu na zargin gwamnatin tarayya ta mayar da wannan mummunan halin da kasar nan take ciki, tamfar wani batu na siyasa, har wannan zargin suke ganin gwamnatin na yi wa batun tabarbarewar tsaron rikon sakainar kashi, ta yadda wai za a yi ta kashe mutnen Arewa, don a samu rage yawansu kafin zaben 2015. Wasu kuma na zargin cewa gwamnatin ta yi biris da batun ne ta yadda zabubbukan za su iya gagara, shugaban kasa ya ci gaba da mulki. Kome ke gaskiyar lamari, maganar dai ita ce rashin adalcin shugabanni daga sama har kasa, ya jefa mu cikin wannan mawuyacin hali, don haka shugabanci nagari ne kadai mafita. Allah Ya ba mu ikon zabar shugabanni nagari