Muna neman tallafi daga gwamnati – Alhaji danladi

Wani dan kasuwa da ke sayar da kayan tireda da kayayyaki irin na fulani a babbar kasuwar Muda Lawan da ke Jihar Bauchi ya bayyana cewa babbar matsalar ’yan kasuwar Arewa-maso-Gabas suke fuskanta ita ce ta rashin jari.dan kasuwar mai suna, Alhaji danladi ya ce ’yan kasuwan yankin sun dauki tsawon shekaru shida suna fama […]

Muna neman tallafi daga gwamnati – Alhaji danladi
Muna neman tallafi daga gwamnati – Alhaji danladi

Wani dan kasuwa da ke sayar da kayan tireda da kayayyaki irin na fulani a babbar kasuwar Muda Lawan da ke Jihar Bauchi ya bayyana cewa babbar matsalar ’yan kasuwar Arewa-maso-Gabas suke fuskanta ita ce ta rashin jari.
dan kasuwar mai suna, Alhaji danladi ya ce ’yan kasuwan yankin sun dauki tsawon shekaru shida suna fama da tashe-tashen hankula wanda ya yi sanadiyyar lakume dimbin rayuwar al’umma.
Ya kara da cewa “tun lokacin da aka rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayun bana muka fara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali domin kowa ya ga yadda hukumomin tsaro suke aiki ba dare ba rana domin murkushe masu ta da kayar baya,” inji shi.
Daga nan ya yi kira da jihohin Barno da Yobe da Adamawa da Gombe da Taraba da kuma Bauchi da su tallafa wa ’yan kasuwa da jari “domin da yawa daga cikin ’yan kasuwa sun cinye jarinsu sakamakon matsalar tsaro da ta addabi yankin a shekarun nan.”

An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Taraba

Jami’an NSCDC sun daƙile harin ’yan bindiga a Kano

Matsalar Tsaro: Ku sayi makamai don kare kanku — Sarkin Argungun

Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki