Muna neman tallafi daga gwamnati –‘Yan kasuwar Kajin k/Wambai
kungiyar masu sayar da kaji a kasuwar kofar Wambai a Jihar Kano sun koka game da rashin samun tallafi daga gwmanati inda suka nemi wannan gwamnati da ta tallafa musu kamar yadda take tallafa wa sauran ‘yan kasuwa a fadin jihar. Alhaji Gambo Naira shi ne Shugaban kungiyar ya shaida wa Aminiya cewa a tsawon […]
kungiyar masu sayar da kaji a kasuwar kofar Wambai a Jihar Kano sun koka game da rashin samun tallafi daga gwmanati inda suka nemi wannan gwamnati da ta tallafa musu kamar yadda take tallafa wa sauran ‘yan kasuwa a fadin jihar.
Alhaji Gambo Naira shi ne Shugaban kungiyar ya shaida wa Aminiya cewa a tsawon shekaru 37 da suka kwashe suna gudanar da kasuwancin kaji a wannan kasuwa ba su taba samun kowane irin tallafi daga gwamnati ba, hakan ya jawo musu rashin ci gaba a harkar kasuwancinsu.
A cewarsa: “Tunda muke a wannan wuri ba mu taba smun tallafi daga gwamnati ba duk kuwa da cewar muna ganin ana tallafawa saran ‘yan uwanmu ‘yan kasuwa. Haka kuma gwamnati ba ta taba zuwa wurinmu ta nuna za ta gyara mana ba. Muna gani aka gyara wa ‘yan uwanmu masu sayar da kaji a kasuwar Tarauni aka zamanantar musu da wurin yanzu haka suna gudanar da sana’arsu a zamance kuma a tsaftace abin ban sha’awa. Duk irin kasuwancin da mutum yake yi idan ya zama ba ya samun tallafi daga gwamnati sai ka ga ya zama.”
Ya ce ’ya’yan kungiyasu na bayar da hadin kai ga gwamnati game da yadda suke biyan kudin haraji a matakai daban-daban ba tare da bata lokaci ba.
“A kullum ‘yan kasuwarmu muna kan gaba wajen biyan haraji, tun daga kan wanda muke biyan jiha har na karamar hukuma. Ba mu bata lokaci wajen biyan haraji” A cewar Shugaban ‘yan kajin wani abu da ke ci wa kasuwnacinsu tuwo a kwarya shi ne ire-iren sababbin gine-ginen shaguna da ake yi a gaban layinsu, wanda hakan ya mayar da su lungu.
“Ada daga bakin titi mutum yake hango layinmu na ‘yan kaji, amma sai ga shi an wayi gari an yi gine-gine a gaban layin namu wanda hakan ya jawo muka shiga lungu, wanda kuma ba karamin dakile kasuwancinmu ya yi ba. Wani lokaci za ka iske kafin a same mu sai mutum yay i ta tambaya kafin ya gane wurin da muke,” inji shi.