Muna rayuwa da wake da garri na kwanaki 68 a gidan yarin Kuje – Masu zanga-zanga

“Mun shafe kwanaki 18 a FCID bayan haka, aka kaimu gidan yarin Kuje. Mun yi kwanaki 68 a gidan yari. Ya kasance mummunan wurin zama kuma ciyarwar da ake yi mana ba tada kyau.

Muna rayuwa da wake da garri na kwanaki 68 a gidan yarin Kuje – Masu zanga-zanga

Masu zanga-zangar da aka sako wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, sun bayyana yadda suke rayuwa da cin wake da garri a tsawon kwanaki 68 da suka yi a gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Aƙalla dai mutane 114 ne da aka kama a zanga-zangar #EndBadGovernance a watan Agusta waɗanda gwamnatin tarayya ta sako su ga gwamnonin jihohin Kano da Kaduna a ranar Talata.

An saki waɗanda aka tsare ga gwamnonin ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, bayan wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja ta sallame su.

Gwamnatin tarayya dai ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa waɗanda ake tuhumar na cin amanar ƙasa ne bayan an kai ga gurfanar da su a gaban kuliya, musamman ƙananan yara a cikinsu.

Da yake zantawa da wakilinmu bayan haɗuwarsu da iyalansu a ranar Laraba, Hassan Muhammad wani mazaunin titin Ghana da ke Unguwar Malali a ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa, ya ce tsare su da aka yi abin ya yi muni matuƙa.

Ya ce, “An kama ni ne a ranar 5 ga Agusta, 2024 a titin Ahmadu Bello da ke Kaduna yayin zanga-zangar #EndBadGovernance. Bayan kama mu, sai aka kaimu sashin binciken manyan laifuka na jihar (CID) inda muka ba da bayaninmu kuma daga nan aka tura mu sashin binciken manyan laifuka na tarayya (FCID).

“Mun shafe kwanaki 18 a FCID bayan haka, aka kai mu gidan yarin Kuje. Mun yi kwanaki 68 a gidan yari. Ya kasance mummunan wurin zama kuma ciyarwar da ake yi ma ba ta da kyau. Suna bamu wake da garri na kwanakin da muka yi a gidan yari.”

Shi ma da yake bayani, Muhammad Abubakar daga Zariya ya ce ya koyi darasi mai ma’ana ta yadda aka kama shi da tsare shi, inda ya ce tsare shi da aka yi za ta kasance abin da zai daɗe yana tunawa na wani lokaci.

Kwamishinar Kula da Ayyukan Jin ƙai da ci gaban jama’a, Hajiya Rabi Salisu ta buƙaci masu zanga-zangar da aka sallame su koma ga unguwanninsu, su riƙa ba da shawarwari wayar da kan jama’a da samar da zaman lafiya domin su kasance nagartattu a cikin al’umma.

Sanata Barau ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano

Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur