Muna samun nasara a Yaki da Cin hanci da Rashawa – Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa na samun nasara a Yaki da cin hanci da rashawa da take yi. Shugaban ya kuma nemi hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa watau EFCC da ta kara kaimi akan nasararorin da ake samu. Shugaban ya bayyana hakan ne a jihar Kaduna, inda ya halarci bikin yaye […]
Shugaba Buhari a wajen bikin yaye jami’a EFCC
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa na samun nasara a Yaki da cin hanci da rashawa da take yi.
Shugaban ya kuma nemi hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa watau EFCC da ta kara kaimi akan nasararorin da ake samu.
Shugaban ya bayyana hakan ne a jihar Kaduna, inda ya halarci bikin yaye jami’an EFCC da suka kammala karatunsu a makarantar sojoji ta NDA.
Shugaba Buhari, ya ce a yanzu Yaki da cin hanci da rashawa na samun yabo daga kasashen waje saboda nasarori da ake ci gaba da samu a kasar.
