Muna sauke nauyin ’yan fansho a kan lokaci – Hukumar Fansho Sakkwato
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa tana a kan gaba da kowace jiha wajen tabbatar da biyan kudaden fansho da garatuti ga ma’aikatan da suka yi ritaya ko barin aiki cikin lokaci ba tare da matsala ba “Dalilin haka ne ya sanya Gwamnati ta kashe Naira biliyan shida, don biyan kudade ga ’yan fansho na […]

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa tana a kan gaba da kowace jiha wajen tabbatar da biyan kudaden fansho da garatuti ga ma’aikatan da suka yi ritaya ko barin aiki cikin lokaci ba tare da matsala ba
“Dalilin haka ne ya sanya Gwamnati ta kashe Naira biliyan shida, don biyan kudade ga ’yan fansho na kananan hukumomin mulki da na jaha a tun lokacin hawan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal bisa karagar mulki.” Shugaban Hukumar Kula da Fanshon Ma’akatan kananan Hukumomi a Jihar Sakkwato, Alhaji Abubakar Umar danlawan Tambuwal ne ya fadi haka a wata hira da manema labarai a garin Sakkwato.
Shugaban wanda kuma shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Kudancin Jihar Sakkwato ya ce Gwamna ya ba su karfin gwiwa don tabbatar da sun samu nasara ga biyan kowa hakkokinsa cikin lokaci; don ganin cewar ba a yi wa kowa coge wajen biyan fansho ko garatuti ba.
Ya ce tun hawansa bisa karagar mulki, Gwamnan ya mayar da hankalinsa ga tabbatar da ayyukan ci gaban jama’a da walwalarsu; mussaman a kan aikin biyan hakkokin ma’aikatan jaha da na kananan hukumomin mulki da suka kunshi malaman makarantar firamare da na manyan makarantu, wadanda suka yi ritaya don ganin ba a hadu da matsala wajen biyansu hakkokinsu a cikin lokaci ba.
“Wannan na daga cikin abin da ya janyo aka samu fahimtar juna da karin ci gaba a Jihar Sakkwato, har kowa yana murna tare da walwala, don ba abin bashi na kowane irin aikin da aka yi na gwamnati a jihar,” inji shugaban na Hukumar Fansho.
A cewarsa, Gwamna yana bayar da isassun kudade, musamman lokacin da Shugaban kasa Buhari ya bayar da tallafi ga jihohin kasar nan domin su biya albashi, ya ce kacokan gwamna ya nemi su biya kowa hakkinsa don kaucewa shiga cikin matsaloli a gaba.
“Yanayin fansho, ka’ida ce wadda muddin ka fara karba, hakika ba za a kore ka ba; don wani dalili sai fa mutuwa ta dauke ka. Sakamakon haka muka mayar da hankali wajen tabbatar da adalci a kan kowa wajen karbar hakkokinsa, mussaman na kananan hukumomin mulki da sauran wadanda abin ya shafa daga fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi”