Muna shan wahalar sana’ar dusa a lokacin damina – Malam Abubakar Sadik
Malam Abubakar Sadik mai sana’ar dusa da kowa (kwalfan wake) da ya dauki tsawon lokaci yana wannan harkar a birnin Sakkwato. “Sana’ar dusa ana shan wahala a lokacin damina. Misali idan aka dauko dusa daga Jihar Neja, idan ruwan sama ya sauka a hanya, ana iya samun asarar buhu 50. “Ni kaina na yi asarar […]
Malam Abubakar Sadik mai sana’ar dusa da kowa (kwalfan wake) da ya dauki tsawon lokaci yana wannan harkar a birnin Sakkwato.
“Sana’ar dusa ana shan wahala a lokacin damina. Misali idan aka dauko dusa daga Jihar Neja, idan ruwan sama ya sauka a hanya, ana iya samun asarar buhu 50.
“Ni kaina na yi asarar buhu 20 kwanan nan. Gashi ba mu taba samun tallafi a wajen gwamnati ba.
“Don haka nake kira da gwamnatin ta tallafa wamasu sana’ar dusa ta hanyar kungiyarsu don kara inganta sana’arsu. Domin su ma suna da gudunmuwa da suke bayar wa a wajen farfado da tattalin arziki,” inji Sadik
Mallam Abubakar ya kara da cewa suna cikin yanayin rashin ciniki don rashin kudi da al’umma ke fama da shi. Kafin sallar layyar bana, ana sayar da buhun dusa dubu 3, amma yanzu ta rage 200 kowa kuma ana sayarwa 4200 amma ta haura har 4500.
Da ya juya kan sha’anin sufuri kuwa cewa ya yi “Ana kawo mana dusa daga Jihar Legas da Ibadan, kowa (kwalfan wake) ana kawo mana daga Salka da Babban Rame da ke Jihar Neja da Bahausa, kuma direbobi na shan wahalar kawo mana kayanmu nan Sakkwato. Muna kira ga gwamnati ta gyara hanyoyin don saukaka sufuri da yawaita arziki ga ‘yan kasa,” in ji shi.
Sadik ya sana’ar cewa harkar dusa akwai riba da faduwa, fatansa dai ‘yan uwansa su rike gaskiya da amana su daina kyashi da hassada don inganta sana’ar su da taimakon gwamnati.