Muna shirin samar da dokar kafa Hukumar Raya Biranen da ke Makwabtaka da Abuja – Sanata Umaru
Sanata Dabid Umaru da ke wakiltar mazabar Neja ta Gabas ya ce suna nan suna kokari domin kafa Hukumar Raya Garuruwan da suke Makwabtaka da Birnin Tarayya, Abuja domin ta rika lura da matsalolin da garuruwan suke fuskanta. Sanata Dabid Umaru ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce […]
Sanata Dabid Umaru da ke wakiltar mazabar Neja ta Gabas ya ce suna nan suna kokari domin kafa Hukumar Raya Garuruwan da suke Makwabtaka da Birnin Tarayya, Abuja domin ta rika lura da matsalolin da garuruwan suke fuskanta.
Sanata Dabid Umaru ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce lura da yadda galibin wadanda suke aiki a Abuja suna zaune ne a wajen birnin kuma babu wani tanadi da aka yi domin bunkasa wadannan garuruwa ya sanya suke kokarin samar da dokar kafa hukumar. “Idan ka duba za ka ga cewa mafi yawan wadanda suke aiki a Abuja suna zaune ne a irin wadannan yankunan kuma babu abin da ake yi wajen kara bunkasa garuruwar kamar samar da hanyoyi da ruwan sha da sauran kayan more rayuwa da za su rage wahalar da jama’a ke sha. Saboda haka muke so a kirkiro wata hukuma da za ta rika lura da wadannan matsaloli ba tare da an tilasta wa jihohin da wadannan garuruwa suke daukar dawainiyarsu ba,” inji shi.
Game da matsalar hare-haren kan bututun mai a yankin Neja-Delta, Sanata Umaru ya shawarci gwamnati ta nemi hanyar da za ta tattauna da maharan ta yadda za a gyara al’amuran. Ya ce idan aka bari abin ya lalace, babu shakka ba zai haifar da da mai ido ba, inda ya ce a irin wannan lokaci ba a amfani da karfi. Ya ce dole a tsaya a saurare su a ga kamun ludayinsu, musamman ganin suna fama da matsaloli masu yawa da suka shafi muhallinsu.
Ya ce aikin kwashe dagwalon mai a yankin da Shugaban kasa ya kaddamar babbar hanya ce ta magance irin matsalolin yankin, kuma shugaban kasa ya yi abin da ya kamata. Ya ce su a majalisa sun bukaci a ci gaba da lallashin ’yan Neja-Delta don a ga yadda za kammala ayyukan da aka fara cikin sauri saboda ta haka ne za a samu dauwamammen zaman lafiya a yankin.