Muna shirya bita kan illar miyagun kwayoyi ga matasa – Bala Fage

Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Ogun, ta ce daya daga cikin matakan da take dauka domin kawo karshen shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa shi ne, shirya taron bita a cikin manya da kananan makarantun jihar.Kwamandan Hukumar Alhaji Bala Fage ya bayyana haka lokacin da suke tattaunawa da […]

Muna shirya bita kan illar miyagun kwayoyi ga matasa – Bala Fage
Muna shirya bita kan illar miyagun kwayoyi ga matasa – Bala Fage

Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Ogun, ta ce daya daga cikin matakan da take dauka domin kawo karshen shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa shi ne, shirya taron bita a cikin manya da kananan makarantun jihar.
Kwamandan Hukumar Alhaji Bala Fage ya bayyana haka lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a Abeokuta, inda ya ce, “A bara, mun yi nasarar shirya taron lacca da wayar da kai har sau 27 a manya da kananan makarantu inda masana suka yi jawabai kan illolin da shan miyagun kwayoyi ke janyowa. Irin wannan taron bita da muke yi a Jihar Ogun yana taimakawa kwarai wajen cusa kyamar miyagun kwayoyin a zukatan matasan.”
Alhaji Bala Fage, ya ce babban kalubalen da suke fuskanta a yanzu shi ne rashin wadatattun kayan aiki musamman motocin sintiri, “Duk da haka a bara hukumar ta yi nasarar kama wiwi mai nauyin kilo dubu 7 da 500 a dajin Erinwo. Kuma mun kama hodar Iblis da koken masu nauyin kilo 112, tare da kama mutum 237 da muke zargi da noman wiwi ko fataucin miyagun kwayoyi. Mutum 220 da aka kama maza ne, a yayin da bakwai mata ne,” inji shi.
Har ila yau ya ce hukumar ta gano wata gona da ake noman ganyen wiwi mai girman hekta 53 inda suka cinna mata wuta ta kone kurmus. Sai kuma wasu kanana da manyan motoci biyar da suka kama ana amfani da su wajen safarar miyagun kwayoyi.
Kwamanda Bala Fage, ya nemi jama’a su taimaka wa Hukumar NDLEA da bayanan da za su taimaka mata wajen kama masu amfani da miyagun kwayoyi a matsayin hanyoyin samun kudi a dare daya ba tare da yadda suke jefa matasa a ciki matsala ba.