Muna so a rika damawa da Hausa Fulani a gwamnatin Borno – Gwandu
Al’ummar Hausawa da Fulani mazaauna Jihar Borno sun kafa kungiyar ci gabansu don ganin gwamnati tana damawa da su, saboda a baya ana nuna musu wariya. Wakilanmu ya tattauna da Sakataren Kungiyar Hausa Fulani ta Jihar Borno, Alhaji Aminu Abubakar Gwandu kan jin inda suka kwana bayan kafuwr kungiyar: Mene ne takaitaccen tarihin wannan kungiya […]
Al’ummar Hausawa da Fulani mazaauna Jihar Borno sun kafa kungiyar ci gabansu don ganin gwamnati tana damawa da su, saboda a baya ana nuna musu wariya. Wakilanmu ya tattauna da Sakataren Kungiyar Hausa Fulani ta Jihar Borno, Alhaji Aminu Abubakar Gwandu kan jin inda suka kwana bayan kafuwr kungiyar:
Mene ne takaitaccen tarihin wannan kungiya taku?
To wannan kungiya tamu ta Borno Hausa Fulani Community Debelopment Association ta samo asali ne daga wata tsohuwar kungiyarmu mai suna Kungiyar Ci gaban Sakkwatawa, Zamfarawa da Kabawa (SOKEZA) mazauna wannan jiha ta Borno, wanda wani dan uwa Malam Yakubu Ahmad BK ya assasata sama da shekara 20, kuma ya agorance ta na tsawon wani lokaci, ni kuma na kasance sakatareta, har zuwa lokacin da aka samu tashin hankalin Boko Haram, wanda ya sa dole muka bar garin. To Allah Ya sa na dawo shi kuma bai dawo ba, sai na ci gaba da jagorancin kungiyar a matsayin Shugaba, sai Alhaji Sa’idu Sale ya zama Sakatare. Duk da cewa akwai wata kungiya da aka kafa mai suna ‘‘Al’umma’’ a wancan lokaci a baya, kungiyarmu ta SOKEZA a gaskiya ta yi tasiri kwarai da gaske domin a lokutan baya mun samu gwamnati ta gina mana makaranta daya, amma ba mu samu hanyoyi da ruwan sha ba kamar yadda muka nema, a wani kauye ana ce masa Zabarmari inda akasarin mutanenmu suke zaune. To amma sai dai ba mu samu wani wakilci a harkar gwamnati ba saboda wani rikicin cikin gida da ya yi mana tarnaki a zamanin mulkin Gwamna Ali Sheriff. Dukkan kungiyoyin da muke kafawa muna kafa su ne da burin ci gaban al’ummarmu, ba don kabilanci ba, sai don hada kan al’ummar Hausa Fulani da suke zaune a wannan jiha da su kansu ’yan asalin jihar ta Borno, wadanda aikin gwamnati ko karatu ko kasuwanci ko noma, ya kawo su nan Jihar Borno don mu zama tsintsiya madaurinki daya, kuma mu bayar da tamu gudunmawar domin ci gaban Jihar Borno. Wannan shi ne a takaice kuma a dunkule manufar kafa wannan kungiya. Na fada maka Kungiyar SOKEZA ta kai shekara 20, to saboda rikicin Boko Haram sai muka yi rauni amma ba mu yi kasa a gwiwa ba sai muka kirkiro da wannan kungiya ta Ci gaban Al’ummar Hausa Fulani mazauna wannan jiha. Muka fadada kuma aka kafa ta a shekarar 2016, wato shakara 3 da suka gabata. Kuma mu ne kungiya ta farko da muka fara yin taron cewa an samu zaman lafiya a Borno bayan Shugaba Buhari ya hau mulki.
Zuwa yanzu mambobi nawa kungiyar take da su?
Ba abin mamaki ba ne idan na ce maka suna da yawan gaske ban san alkaluman mambobin wannan kungiya ba, saboda duk wani mai amsa sunan Hausa Fulani yana cikinta har ma wadanda ba Hausawan ba wato misali mutanen Gwoza da Biu da kuma wadansu baki daga wasu wuraren duk sun shiga wannan kungiya ta Hausa Fulani saboda tasirinmu da yawanmu da kuma zamantakewarmu saboda haka muna da yawan gaske.
Ko wannan kungiya taku tana yin ayyukan taimakon kai-da -kai don tallafa wa juna?
Kwarai kuwa muna taimaka wa juna ta kowace fuska, domin wannan ne ofishinmu kuma a ciki muke yin tarurrukan duba lamuran kowa tare da sanya haraji ga kawunanmu idan wani na bukatar taimakon gaggawa, tare da gudanar da aikin agaji na taimaka wa marasa karfi da gajiyayyu wadanda suke bukatar taimako ko da ba a cikinmu ba. Don bai dade ba muka gama aiki a gidan kurkuku na Madimum Security Prison da ke nan Maiduguri, inda muka koyar da sana’o’i ga mazauna gidan don ya zamo kafin su fita su koyi san’o’in hannu. Mun koyar wa wadansu sana’ar dinkin keke wadansu aski na zamani da sakar hannu ga mata da kafinta da walda da yadda ake yin takalma da sauransu don idan suka fita su rika dogaro da kawunansu. Kuma mutanen da muka koya musu wadannan sana’o’i a gidan kurukukun suna da yawa, sai da muka hada hannu da Makarantar Future Probince ta Barista Zanna inda aka raba masu koyon gida biyu, rabi aka yi musu a wancan makarantar rabi kuma aka yi musu a gidan kurukukun.Hakazalika mambobin kungiyar na Unguwar Gwange sun taimaka wajen maido da yara makaranta, har guda 250, suka dinka musu rigunan makaranta da takalma da jakunkuna duk suka komar da su makarantun firamaren da suke Gwange, kuma har gwamnatin jiha ta tura wakilanta, Hukumar Wayar da Kai ta Kasa (NOA), ta tura wakilanta, shugabannin ilimi na kananan hukumomin da abin ya shafa duk sun tura wakilansu wajen taron.
Ta wacce hanya kuke samun kudade har kuke tafiyar da ayyukanku?
Muna da hanyoyin samun kudaden shigarmu na cikin gida guda biyu, na farko shi ne mukan yi wa sababbin shigowa kungiya katin shaidar zama dan kungiya, akwai kudin da mutum yake bayarwa sai mu yi masa irin tsarin da ya dace mu yi masa. Kuma muna dora wa kawunanmu ’yan kudin da mutum zai bayar zuwa wani lokaci musamman masu hannu da shuni a cikinmu. Idan za mu gudanar da wasu muhimman ayyuka sai mu shaida musu ga irin ayyukan da za mu yi ga kasafinmu saboda haka muna bukatar agaji sai su agaza mana. Sannan muna aza wa kanmu haraji a tarurrukan da muke gabatarwa. Wadannan su ne hanyoyin da muke samarwa da kungiya kudaden shigarta da sauran wasu hanyoyi.
A lokutan baya al’ummar Hausawa da Fulani mazauna Borno za a iya cewa ana nuna musu bambanci ko kun fuskanci wannan matsala bayan kafa kungiyar taku?
Lokacin da muka kafa Kungiyar Hausa Fulani, wariyar ta ragu sosai, to amma a lokacin da muka yi SOKEZA ne muka samu wannan matsala amma shi ma da muka dage a kan gaskiya saboda kundin tsarin mulkin kasa ya ba kowa ’yancin kafa kowace kungiya, to mun jure mun yi kuma mun samu nasarori da yawan gaske.
Wane kalubale kuka fuskanta kuma ta yaya za ku magance wannan kalubale?
Wato kalubalen da muka fuskanta a baya shi ne na rashin fahimtar mabiya, yau mabiya sun gano cewa ashe bangaren da Sakatare Janar ya tsaya kai-da-fata cewa ba zai hada kai da wadancan ba shi ne na gaskiya.
Su wane kake nufi?
Su bangaren da suka balle ko kuma wadanda muka kore su. Ba sai mun fadi suna ba, amma su mambobinmu sun san su.
To a yanzu menene matsalar kungiya?
Matsalar Kungiyan da ya yi mana tarnaki kuma muke fuskantarsa shi ne na rashin taro da kwabo, wanda ya shafi kowa don bamu kadai yake damun muba, hattama ita da kanta gwamnati tana kuka da matsalar tattalin arziki, saboda haka in zamuyi abu sai mun shirya kafin muyi shi, to kuma yakan dauki lokaci kafin a tara adadin kudin da ake bukata ayi amfani dashi.’’
A karshe wane kira kake da shi ga al’umma da wadanda suka balle don su zo a hadu a tafi tare?
Kiran da zan yi musu shi ne su tuna rantsuwar da suka yi a gaban al’umma wadda Allah ne shaida, sai kuma mutanen da suke zaune a wancan lokaci, sun yi rantsuwa da Allah da girman Allah da Alkur’ani cewa ba za su yarda a hada kai da su a cuci al’umma ba ko a yaudare su ba. To su tuna da wannan rantsuwa, don al’umma na nan tana kallonsu da wannan rantsuwa muna jira mu ga sakamakon rantsuwar nan, sannan su ji tsoron Allah su tuba su dawo hanya wadda take ita ce daidai kamar yadda jama’a suka shaida. Domin abu biyu ne ke hallakar da dan Adam a duniya, na farko jahilci, na biyu son zuciya. To mafi yawansu sun gane gaskiyar lamarin amma son zuciya ta hana su su dawo hanya ta gaskiya muna fata su yaki wadannan cututtuka biyu jahilci da son zuciya.
Mece ce fatarka ga wannan kungiya?
Fatata mu samu dawwamammen zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa, ta yadda al’ummarmu ta Hausa Fulani za su mori mulkin dimokuradiyya. Shi kuma Gwamna Babagana Umara, ya fahimci cewa mu ma abokan tafiya ne kuma abokan aiki, kuma za mu yi aiki don amfanin al’umma ba don bukatun kanmu ba, don haka ya tafi tare da mu.