Muna so a yafe wa Nijeriya basussuka —Kashim Shettima
Idan ƙasashe ba su tashi tsaye ba, babu ƙasar da ba za ta iya fuskantar illolin sauyin yanayi ba.
Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta mayar da hankali wurin ganin an yafe wa Nijeriya da sauran ƙasashe masu tasowa basussukan da ake binsu.
Sanata Kashim Shettima wanda ke wakiltar Shugaba Bola Tinubu, ya faɗi hakan cikin jawabinsa a gaban Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a taronta da ke gudana a birnin New York na Amurka.
Ya bayyana cewa “Dole ne mu tabbatar da cewa duk wani sauyi da za a kawo ga tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa ya haɗa da tsarin sauƙaƙa bashi, domin bayar da damar samun ci gaba mai ɗorewa ta ɓangaren kuɗi.
“Ƙasashen da ke kudancin duniya ba za su samu wani ci gaban tattalin arziki ba, ba tare da rangwame na musamman ba da kuma nazarin nauyin bashin da suke ciki a halin yanzu,” in ji Shettima.
Sauran batutuwan da mataimakin shugaban ya taɓo a jawabin nasa sun haɗa da neman haɗin kan Majalisar Ɗinkin Duniya wajen ganin an mayar da kuɗaɗen sata da waɗanda aka fitar da su zuwa manyan ƙasashe ba bisa ƙa’ida ga ƙasashen da aka sato su.
Dimokuraɗiyya na fuskantar barazana a Afirka
Daga cikin abubuwan da ya soma magana a kansu a gaban taron na MDD, akwai batun yadda dimokuraɗiyya ke fuskantar barazana musamman a Yammacin Afirka.
Ya bayyana cewa a kwanakin baya Nijeriya ta cika shekara 25 da ɗorewa kan turbar dimokuraɗiyya haka kuma an shafe sama da shekara 20 Afirka na kan turbar dimokuraɗiyya.
“Sai dai sauya gwamnati ba tare da bin ƙa’idar kundin tsarin mulki ba da ƙwace gwamnati da ƙarfin soji a wasu ƙasashen yankin Sahel ya nuna yadda dimokuraɗiyya ke da rauni idan babu cikakken ci gaban tattalin arziƙi da zaman lafiya da tsaro.
“Wannan rauni ne ba wai ci gaban gwamnatin dimokuraɗiyya a Afirka ba, ya kamata a mayar da hankali a kai a tattaunawarmu a wannan da sauran ɓangarori na wannan taron na Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya,” in ji Shettima.
A bai wa Falasɗinu ’yanci
“A yau, dukanmu mun shaida irin hali mai sosa zuciya da ake ciki a Gaza da sauran sassan Falasɗinawa.
“Ba za mu iya tattauna batun yaƙi da zaman lafiya da sulhu ko jinƙai ba tare da taɓa batun rikicin Isra’ila da Falasɗinawa ba wanda aka soma tun daga 7 ga Oktobar bara.
“’Yanci wani haƙƙi ne da ba za a tauye shi ba, kuma haƙƙi ne wanda ba za a iya hana shi ga kowa ba.
Al’ummar Falasɗinu sun cancanci ‘yancin kansu. Sun cancanci samun gida na kansu a yankunan da wannan Majalisar ta amince da su da kuma dokokin ƙasa da ƙasa, wanda aka yi watsi da su,” in ji Shettima.
A faɗaɗa Kwamitin Tsaro na MDD
Kashim Shettima ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta kawo sauyi ga kwamitin tsaronta da kuma faɗaɗa shi ta yadda za a samu ƙarin ƙasashe da za su zama mambobi na dindindin da waɗanda ba na dindindin ba.
“Kawo sauyi ga kwamitin tsaro na da muhimmanci idan MDD na son ta ƙara ƙarfafa dacewarta da amincinta a cikin duniyarmu mai saurin canzawa.
“Wasu masu kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun bayar da ƙwarin gwiwa da goyon baya kan batun sake fasalin majalisar,” in ji Shettima.
“Akwai buƙatar faɗaɗa kwamitin tsaron, ta ɓangaren rukunin mambobi na dindindin da waɗanda ba na dindindin ba, don nuna bambance-bambance da yawa na duniya.
“Muna ba da cikakken goyon baya ga kokarin Sakatare-Janar Guterres game da wannan.
Sauyin Yanayi
“A ‘yan makonnin da suka wuce, ambaliyar ruwa ta shafe wurare masu yawa a ƙasata, daga ciki har da ɗaya daga cikin birane mafiya girma a Arewa Maso Gabas, Maiduguri.
“Akwai wasu sassa na Nijeriya da su ma suka fuskanci bala’o’i da asarar rayuka da dukiyoyi,” in ji Shettima.
Saboda haka Kashim Shettima ya buƙaci gaba ɗaya ƙasashe da a tuna irin alƙawuran da aka yi a yayin tarukan da ake yi na sauyin yanayi a duk shekara da kuma aiwatar da su.
Ya bayyana cewa idan ƙasashe ba su tashi tsaye ba wurin aiwatar da waɗannan alƙawuran, lallai babu ƙasar da ba za ta iya fuskantar illolin sauyin yanayi ba.