Muna son a haramta auren mace fiye da 1 a duniya —MDD

An haramta auren mace sama da guda a kasashen duniya da dama.

Muna son a haramta auren mace fiye da 1 a duniya —MDD

Wasu mata ‘yan Matan Indonesia dake adawa da auren mace fiye da 1 a tsakiyar birnin Jakarta, a ranar 24 ga Nuwamba, 2000. © REUTERS/Darren Whiteside

Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar da ke yaki da cin zarafin da ake yi wa mata na bukatar haramta auren mace sama da guda daya saboda abinda suka kira kare ’yancin mata a duniya.

Alkaluman hukumar sun nuna cewar kashi 2 ne kacal na al’ummar duniya ke zama a gidajen da ake da mata sama da guda, kamar yadda wani binciken da Cibiyar Pew da ke Amurka ta gudanar a kasashe 130 da kuma wasu yankuna.

Rahotan ya ce an haramta auren mace sama da guda a kasashen duniya da dama, ciki har da nahiyar Turai, amma kuma matakin ya halasta a kasashen Gabas ta Tsakiya da Asia da kuma wasu yankunan Afirka.

Sakamakon binciken da aka gudanar ya ce an fi samun auren mata da yawa a yankin Afirka da ke Kudu da sahara, inda kashi 11 na al’ummar yankin suka fito daga gidajen da ake auren mata da yawa.

Binciken ya ce kashi 36 na al’ummar Burkina Faso na da mata sama da guda, yayin da ake da kashi 34 a Mali, sai kashi 30 a Gambia sannan kashi 29 a Jamhuriyar Nijar.

RFI ya ruwaito cewa alkaluma sun nuna cewar kashi 28 na al’ummar Najeriya ke da mace sama da guda, yayin da Guinea ke da kashi 26.

Binciken ya nuna cewar an fi samun auren mace sama da guda a tsakanin al’ummar Musulmin Afirka, sabanin yadda ake samu daga Kiristoci.