Muna taimakawa wajen samar da zaman lafiya – Sarkin Fulani

Sarkin Fulanin Shagamu kuma mataimakin shugaban sarakunan Fulani na kasa, Alhaji Salisu Garba ya bayyana irin muhimmiyar rawa da kungiyarsu ta sarakunan Fulani makiyaya na Kudu masu yamma suke takawa wajen samar da zaman lafiya tsakanin al’ummarsu da kungiyoyin manoma da sauransu, ba na Kudu maso yamma kadai ba, duk yankunan jihohin Kudancin Najeriya. Sarkin […]

Muna taimakawa wajen samar da zaman lafiya – Sarkin Fulani
Muna taimakawa wajen samar da zaman lafiya – Sarkin Fulani

Sarkin Fulanin Shagamu kuma mataimakin shugaban sarakunan Fulani na kasa, Alhaji Salisu Garba ya bayyana irin muhimmiyar rawa da kungiyarsu ta sarakunan Fulani makiyaya na Kudu masu yamma suke takawa wajen samar da zaman lafiya tsakanin al’ummarsu da kungiyoyin manoma da sauransu, ba na Kudu maso yamma kadai ba, duk yankunan jihohin Kudancin Najeriya.

Sarkin ya bayyana irin rawar da wannan kungiyarsu ta sarakunan take takawa wajen sulhu tsakanin al’ummar Fulani da manoma. “Ba a yanzu kadai ba da wannan kungiyarmu take irin wannan ayyukanta na ganin ta samar wa alummar Fulani ci gaba da zaman lafiya tsakaninsu da kungiyar manom ta nan Kudu maso yamma da sauran yankunan tun shekaru da dama da suka wuce, wannan kungiyar tamu ta sarakunan Fulani ta kasa, a gaskiya take taka muhimmiyar rawa kwarai, musamman a Kudu maso yamma, domin a duk lokacin da aka samu wata matsala ta faru muna zuwa mu tsaya da gaskiya har sai mun ga mun warware ta ko mu kira taro na musamman na sarakunanmu da hadin kan jama’armu sai mu zauna da masu gonaki kuma a wani zubin ma har zaman yana kai mu mu zauna da wasu gwamnoni domin tattaunawa a kan muhimman batutuwa da suka shafi Fulanin da manoma a yankunan kuma da wannan muna samun maslaha.” Inji shi.
Daga nan kuma sai ya shawarci al’ummar Fulani makiyayan da cewa su zauna lafiya da kowa a kasar nan. Su kasance masu hakuri da juna kuma idan wani abu ya faru kada su ce za su dauki doka a hannu. “Abin da za ku yi shi ne, ku rika neman shawara daga magabata, masu hangen nesa cikin ilimi da basira, domin sasantawa.”
Sarkin kuma ya shawarci ita sabuwar gwamnati a kan batun Fulani makiyaya a kasar nan, wadanda suka dade suke fama da wahalar rayuwa tsakanin al’ummar Najeriya na tsawon shekaru goma sha shida, cewa gwamnatin da ta dube su da idon rahama. Ya nemi da a kikiro musu da hukuma ta musamman mai kula da sha’anin makiyaya.