Muna umartar Rasha ta gaggauta dakatar da mamaya a Ukraine —Kotun Duniya

Mai shari’a Joan Donoghue ya bayyana kotun ta ICJ a matsayin fadar tabbatar da adalci.

Muna umartar Rasha ta gaggauta dakatar da mamaya a Ukraine —Kotun Duniya

Kotun Duniya da ke Hague a Holland

Kotun Duniya da ke birnin Hague a Holland ta umarci Rasha ta gaggauta dakatar da mamayar da ta ke yi wa Ukraine, daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ita ma a bangare guda ke sake mika rokonta ga Rasha wajen ganin an kawo karshen yakin tare da warware rikicin ta lumana.

Hukuncin kotun na ICJ da ke biyo bayan karar da Ukraine ta shigar ranar 27 ga watan Fabarairu kwanaki 3 bayan mamayar da Rasha ta fara yi mata ya umarci Moscow ta janye dakarunta daga sassan Kiev cikin sauri, a kokarin tabbatar da zaman lafiya tsakaninta da makwabciyartata.

Hukuncin kotun wanda babu tabbacin ko Rasha za ta mutunta shi, na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun kasar ke ci gaba da yi wa manyan biranen Ukraine kawanya kamar yadda Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito.

Tuni Ukraine ta bayyana hukuncin na ICJ da gagarumar nasara yayin da ta sha alwashin ci gaba da matsa kaimi har zuwa lokacin da Rashan za ta janye tare da dawowar zaman lafiya a sassan Kiev da kewaye.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce zuwa yanzu fararen hula fiye da miliyan 3 ne suka yi kaura daga yankunan da Moscow ta yi wa mamaya don tsira da rayukansu daga hare-haren Sojin, wanda kuma hukumar kare hakkin dan adam ta MDD din ke cewa zuwa yanzu ya hallaka fararen hula dubu 1 da 834.

Mai shari’a Joan Donoghue da ya jagoranci zaman shari’ar na yammacin Laraba, ya bayyana kotun ta ICJ a matsayin fadar tabbatar da adalci yana mai nuna damuwa da yadda Rasha ke amfani da karfin Soji a rikicin maimakon warware shi ta ruwan sanyi.

Bayanai sun ce ICJ ta zartas da hukuncin ne ba tare da halartar wakilcin Rasha a zaman shari’ar ba.

Cikin hujjojin da Ukraine ta kafa wajen shigar da karar gaban kotu shi ne zargin Rasha da kokarin kisan kare dangi kwatankwacin na shekarar 1948 batun da tuni Moscow ta musanta yayin zaman sauraren shari’ar na ranakun 7 da 8 ga watan da muke ciki bisa cewa babu hujjar da ke tabbatar da zargin.

Rasha dai na ci gaba da nanata cewa, matakinta na amfani da Soji a Ukraine kokari na kare kanta daga barazanar tsaron da ta ke fuskanta daga makiyanta da kungiyar tsaro ta NATO.