Muna neman Kwankwaso ya dawo PDP —Damagun
Damagun ya ce har yanzu PDP ba ta cire tsammanin cewa Kwankwaso zai sake dawowa cikinta ba
Jam’iyyar PDP ta ce nan ba da jimawa na za ta nemi tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake dawowa cikinta.
Muƙaddashin Shugaban PDP na Ƙasa, Umar Iliya Iliya Damagun ne ya ce jam’iyyar za ta yi zawarcin Kwankwaso ya sake dawo cikinta ne domin ganin yadda za ta ƙwace mulki daga hannun Jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.
Damagun ya sanar da haka bayan Kwankwaso a wata hira da BBC ya bayyana cewa babbar jam’iyyar adawar ba za ta iya sake nasara a zaɓen shugaban kasa ba, saboda ta riga ta mutu.
Ya ce, “Nan ba da jimawa ba za mu tuntuɓi Kwankwaso, kuma har gobe ba ma cire tsammanin zai iya zuwa PDP, a yi tafiya da shi mu karkaɗe jam’iyyarmu mu fuskanci wannan azzalumar gwamnati.”
- Shari’o’in da suka tayar da ƙura a 2024 a Najeriya
- Karɓa-karɓa: Ban taɓa ƙulla yarjejeniya da Atiku ba —Kwankwaso
- NAJERIYA A YAU: Yadda taƙaddama ta kanannaɗe siyasar ƙananan hukumomi a 2024
Bayanin shugaban tsohuwar jam’iyya mai mulkin na zuwa ne kimanin awa 24 bayan Kwankwaso ya caccaki da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasanta a zaɓen 2023, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, kan abin da ya kira ƙagen ƙulla yarjejeniyar karɓa-karɓar mulki tsakaninsu da Peter Obi na Jam’iyyar LP.
Ambasada Damagun ya gaskata zargin da Kwankwaso ya yi cewa cin fuskar da aka yi musu a PDP ne ya sa suka sauya sheƙa. Ya ce shi kansa ya yi iya koƙarinsa a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar a lokacin domin ganin ba su fice ba amma abin ya faskara.
Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za su tuntuɓi Kwankwaso, duk da cewa sun san ya riga ya fusata; amma ya san cewa da wuya ya cim ma burinsa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar da ya koma.
Ya jaddada cewa PDP a shirye take ta karɓi Kwankwaso da duk tsofaffin mambobinta da suka bar ta saboda ɓacin rai da sauran abubuwan da suka faru a baya.
Damagum ya ce “Duk da haka ba shi da Jam’iyyar da ta fi PDP domin idan ka duba ita ta rene shi, ita ta kawo masa siyarsa ta kai inda yau ta kai, har gobe ba ma cire tsammani zai iya zuwa a yi tafiya da shi, mu karkaɗe jam’iyyarmu mu fuskanci wannan azzalumar gwamnati,” in ji shugaban.
‘Kwankwaso bai yi wa kansa adalci ba’
Duk da haka shugaban na PDP ya bayyana cewa, duk da cewa Kwankwaso na da ’yancin fadar ra’ayinsa kan yadda yake ganin PDP, amma tsohon Gwamnan Kanon ya tuna cewa, idan har PDP ba ta mutu a 2015 lokacin da suka fice daga cikinta, “a lokacin da suke ganin sun yi mata illa, to ban ga dalilin da za a ce ta mutu ba yanzu.
“Kuma kar ka manta jam’iyyar PDP ita kaɗai ce ke iya cin zaɓe idan aka cire masu mulki.”
Damagun ya ce shi kansa Kwankwason da ya ce PDP ta mutu, ai bai yi wa kansa adalci ba, domin ai ya ɗauki jam’iyya amma jiha nawa ya ci?
Ya kuma yi tutiya da cewa PDP ce kaɗai ta iya lashe zaɓen shugaban ƙasa a tsawon shekara 25 da suka gabata a Najeriya, in banda APC mai mulki a yanzu.
Sannan kuma PDP ce kaɗai Jam’iyyar adawa da ke da gwamnoni da sanatoci da sauran zaɓaɓɓun shugabanni a kowane yankin ƙasar nan. Hasali ma ya ce idan aka cire PDP, jam’iyyu huɗu ma idan aka haɗa su, ba za su iya cin zaɓe ba.
Kuma ita ce kaɗai a ƙasar ta shafe waɗannan shekaru ba tare da ta sauya sunanta ba.