Munafunci da rashin karbar shawara ya sa muka fice daga PDP – Abdullahi Adamu
A ranar Asabar din makon jiya ne tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, Sarkin Yakin Keffi ya gana da manema labarai don murnar cikarsa shekara 70 a duniya. Wakilinmu ya zanta da shi kan gwagwarmayarsa a fagen siyasa da sauransu: Aminiya: Yallabai yaya harkokin siyasarka suka faro? Sanata Adamu: Na fara shiga harkar siyasa […]
A ranar Asabar din makon jiya ne tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, Sarkin Yakin Keffi ya gana da manema labarai don murnar cikarsa shekara 70 a duniya. Wakilinmu ya zanta da shi kan gwagwarmayarsa a fagen siyasa da sauransu:
Aminiya: Yallabai yaya harkokin siyasarka suka faro?
Sanata Adamu: Na fara shiga harkar siyasa ce daga shiga zaben kwamitin gyaran tsarin mulkin Najeriya a 1978, na shiga zabe a nan gida Keffi Allah ya ba ni nasara na tafi Legas. A can ne na hadu da irin su Mai girma tsohon Shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari da su marigayi Abubakar Rimi da sauransu. Kuma saboda ’yan wasu rikice-rikice da ake samu a wannan majalisi ya kai ga aka kafa kungiya ta Tarayyar Najeriya, to kafin a gama aikin tsarin mulki ne wannan kungiyar da muka kafa ta haifi Jam’iyyar NPN, cikin ikon Allah na kawo NPN Jihar Filato na zama sakatarenta na farko kuma dan babban kwamitinta na kasa. Ana cikin haka aka zo aka yi zaben 1979, NPN ta ci a sama da mafi yawan jihohi amma a Filato NPN ta fadi. A tsakanin 1981 zuwa1982 sai Allah Ya sa na zama Shugaban Jam’iyyar NPN na Jihar Filato. Bayan rusa mulkin farar hula na koma makarantar lauyoyi har na zama babban lauya domin a lokacin ina daya daga lauyoyin Najeriya da Kotun koli ta san da zamansu. A zamanin gwamnati Janar Sani Abacha aka nada ni Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje daga 1994-1997, kuma bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999, sai na tsaya takara kuma Allah Ya ba ni sa’a na zama Gwamnan Jihar Nasarawa, sai a shekara ta 2003 na zarce karo na biyu, bayan shekara takwas ina Gwamna, sai na nemi tsayawa takarar Shugaban kasa a lokacin tare da marigayi Shugaban kasa Umaru ’Yar’aduwa Allah bai ba ni ba. Daga nan sai na zama Sakataren Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP ta kasa a lokacin Cif Olusegun Obasanjo ne Shugaban Kwamitin. Sai kuma al’umma suka nemi in tsaya takarar Sanata a shekara 2011, na tsaya Allah Ya ba ni nasara har ya kai ga zaben shekarar 2015 na sake tsayawa takarar Sanata a Jam’iyyar APC kuma Allah Ya ba ni nasara yanzu haka ni ne Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattawa.
Aminiya: Ganin Jam’iyyar PDP ta kai ka matsayi da ka samu a siyasa ka zama sanata karo na farko, me ya sa ka juya mata baya, ka canza sheka zuwa Jam’iyyar APC?
Sanata Adamu: Idan aka yi batun PDP babu shakka mu muka kafa PDP ranar 30-11 1998 a tsohon filin fareti na Abuja. Ni aka ba ni tutar Jihar Nasarawa na zo na tsaya takara a cikinta kuma na ci zabe na zama Gwamna na zama Sakataren Kwamitin Amintattu wanda duk abin da za a yi a PDP a kasar nan sai an tuntube mu, amma a karshe sai muka fahimci cewa akwai munafinci da kin jin shawara a cikin jigogin jam’iyyar ta PDP. Domin ni da kaina samu tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ba sau daya ba, ba sau biyu ba domin mu san yadda za a gyara Jam’iyyar PDP amma abin ya ci tura. Hakan ya sa ni da wadansu irina muka yanke shawarar barin jam’iyyar kuma dafin da muka kafa mata na nan na bin ta har abada.
Aminiya: Me za ka ce game da yadda Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shigo da shinkafa ta iyakokin kasa, wanda ya yi sanadiyar tsadar kayan abinci a Najeriya?
Sanata Adamu: Idan za abi ta tawa kodayake abin da zan fada ba zai yi wa wadansu dadi ba, amma a yi mini gafara kuma a yi hakuri. Muddin za ci gaba da bari ana kawo abinci daga kasar waje, to har abada ba za mu magance abin da ke damunmu ba, saboda haka dole mu yi hakuri mu yi amfani da abincin da ake nomawa a kasarmu. Idan aka yi batun shinkafa, ko can baya shinkafa ba abincin kullum ba ce inda za ka ga sai ana bikin Sallah ko suna ko aure ake amfani da shinkafa. Kuma ba za a ce mutumin yanzu ya fi na da lafiya ba, yanzu saboda yawan shigo da shinkafa hakan ya sa lalaci a zukatan ’yan Najeriya, ba su son yin noma kuma sun mance da abincinsu na gargajiya. Idan aka yi batun dan Arewa ai sai dambu ko mandako ko dakuwa ko dan wake da sauransusu da yanzu an mance da su an koma cin shinkafa. Shinkafar ma ta wata kasa inda muke azurta wasu kasashe muna talauta kanmu. Saboda haka shawarata ita ce mu kara hakuri mu ci gaba da cin abin muke nomawa zuwa wani lokaci bayan wuya sai dadi insha Allahu.
Kuma ina ja hankalin manyan mutane masu hannu da shuni su fadada harkar namo da kiwo domin haka ne kadai shi zai kawo karshen tsadar abinci a kasar nan ba bude iyakoki ba.