Munanan hare-hare 12 da aka taba kai wa gidajen yari a Najeriya
Tun a 2010 ne aka fara kai harin gidajen yarin
Hare-hare a gidajen yari na daga cikin matsalolin da Najeriya ke fama da su sakamakon rashin tsaro.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren da ’yan bindiga suka kai a wasu gidajen yarin kasar, sun yi sanadiyar tserewar fursunoni su sama da 7,000 kawo yanzu.
- Sallah: Ganduje ya ba makarantun Kano hutun kwana 10
- Zargin Batanci: Lauyan Abduljabbar ya fice daga kotu a fusace
Daya daga cikin munanan hare-haren da aka taba kai wa a Najeriya shi ne na kurkukun Kuje da ke Abuja na ranar Talata, wanda daruruwan fursunoni, ciki har da kasurguman mayakan ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP, suka tsere.
Aminiya ta yi nazari a kan jerin wasu hare-haren da aka taba kai wa gidan yarin kasar tun daga 2010:
- Gidan yarin Bauchi
Wannan harin ya faru ne a ranar bakwai ga watan Satumban 2010, kuma maharan da ake zargin mayakan Boko Haram su sama da 50 ne suka kai harin wanda ya yi sanadiyar tserewar fursunoni 721. Mutum biyar sun rasu sannan shida sun ji rauni.
- Gidan yarin Ogun
Hari ne da aka kai gidan yarin da ke Shagamu a Jihar Ogun a ranar hudu ga watan Janairun 2013.
Fursunoni 20 ne suka tsere sannan jami’ai da wasu fursunonin suka ji rauni.
- Harin gidan yarin Ondo
Harin ya auku a ranar 30 ga Yunin 2013 a gidan yarin Olokuta da ke yankin Akure, Jihar Ondo.
Wasu ’yan bindiga da aka yi zargin ’yan fashi ne suka kai harin, wanda ya yi silar tserewar fursunoni 175 da mutuwar mutum biyu da kuma jikkata wani.
Amma an samu nasarar sake damke 54 daga cikin fursunonin da suka gudu yayin harin.
- Gidan yarin Legas
A ranar 10 ga Oktoban 2014, wasu fursunoni suka yi yunkurin fasa gidan yarin Jihar Legas amma hakan ya ci tura.
Sai dai yamutsin ya yi sanadin mutuwar fursunoni 20 tare da jikkata 80, sannan wasu 12 sun tsere.
- Gidan yarin Kogi
A ranar 2 ga Nuwamban 2014 mahara da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai hari gidan yarin da ke Koton-Karfe a Jihar Kogi.
Fursunoni 144 ne suka tsere a harin, sannan daya ya mutu amma daga bisani an sake damke 45 daga cikin wadanda suka gudun.
- Harin gidan yarin Ekiti
Kimanin ’yan bindiga 60 ne suka kai hari gidan yarin tarraya da ke Ado Ekiti, Jihar Ekiti a ranar 30 ga Nuwamban 2014.
Harin ya bai wa fursunoni 341 damar tserewa, jami’i daya ya rasa ransa, sannan an sake kama 10 daga cikin fursunonin da suka arce.
- Gidan yarin Minna
Shida ga Disamban 2014, ita ce ranar da wasu ’yan bindiga uku suka kai hari gidan yarin Minna a Jihar Neja.
Fursunoni 270 ne suka tsere sannan jami’i daya ya ji rauni, amma babu asarar rai ko guda.
- Gidan yarin Kuje
Harin ya faru ne ranar 24 ga Yunin 2016 a gidan yarin Kuje da ke Abuja, inda wasu manyan fursunoni biyu suka tsere — Solomon Amodu da Maxwell Ajukwu — wadanda baki dayansu suke zaman jiran hukunci a wancan lokaci.
Haka nan, an sake yinkurin fasa gidan yarin na Kuje a ranar 29 ga Agustan 2016 inda fursunonin da ke ciki suka nemi ta da yamutsi, amma jami’ai sun hanzarta samar da daidaito.
- Gidan yarin Owerri
An kai harin ranar 5 ga Afrilun 2021, inda mahara da ake zargin mambobin reshen kungiyar IPOB ta ESN ne a Jihar Imo suka far wa gidan yarin Owerri.
Fursunoni 1,844 ne suka arce a harin.
- Gidan yarin Edo
Wani gungun mutane da suka fake da zanga-zangar EndSARS sun kai farmaki gidan yarin Benin City da na Oko a Jihar Ondo, duk a ranar 19 ga Oktoban 2020.
Lamarin da ya yi sanadin tserewar fursunoni 1,993 tare da wawushe kayayyakin gwamnati hade da makamai.
- Gidan yarin Filato
An kai harin ne a ranar 28 ga Nuwamban 2021, harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 10 tare da jikkata da dama. Fursunoni 262 ne aka ce sun gudu a sakamakon harin, sannan an sake kamo 10 daga ciki.
- Gidan yarin Kuje
Wannan shi ne hari na baya-bayan nan da aka kai gidan yari a Najeriya, inda a ranar 5 ga Yulin wasu mahara suka kai farmaki gidan yarin.
Ana fargaban fursunoni 900 sun gudu sakamakon harin, kodayake Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya ta ce an sake damke 551 daga cikin fursunonin da suka gudun.