Munfukan Arewa ke fara bata shugaban da ya fito daga yankinsu – Danmalikin Kebbi
Aminiya: Me za ka ce game da wadansu ’yan Arewa na kusa da Shugaba Buhari da suka fara fitowa suna cewa ba za su mara masa baya ba a zaben badi, inda wadanda ba ’yan Arewa ba suka fara mara musu? danmalikin Kebbi: Duk gwamnatin da ka ga ana yi mata zagon kasa a Najeriya, […]

Aminiya: Me za ka ce game da wadansu ’yan Arewa na kusa da Shugaba Buhari da suka fara fitowa suna cewa ba za su mara masa baya ba a zaben badi, inda wadanda ba ’yan Arewa ba suka fara mara musu?
danmalikin Kebbi: Duk gwamnatin da ka ga ana yi mata zagon kasa a Najeriya, ta mutumin Arewa ce. Kuma munafikan Arewa ne suke fara bude kofa a ci mutuncin duk wata gwamnati ta dan Arewa a kasar nan. Yau a Najeriya akwai wadansu mutane da suka fito suna fadin maganganun da suka ga dama, suna kuma rubuce-rubuce. Dama tun daga fara kiran sunayen wadannan mutane a cikin gwamnati, mutane suka fara cewa za a samu matsala saboda mafi yawansu masu laifi ne, domin sun aikata barna a baya. Wadannan mutane da Shugaba Buhari ya dauko ya ba su amana a cikin gwamnatinsa sun ci amanarsa. Daga cikinsu akwai minstoci da wadansu da ke kusa da shi, ya kamata su sauka daga kan mukamansu maimakon su rika cewa idan zai sake tsayawa takara ba za su goyi bayansa ba. Bai kamata wannan gwamnati ta ci gaba da barin irin wadannan mutane da suka azabtar da ’yan adawa a zamaninsu su ci gaba da zama a cikin gwamnatin ba, domin za su ci gaba da yi mata zagon kasa, saboda ba sa tare da ita.
Aminiya: Me za ka ce game da wasikar da Cif Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Buhari?
danmalikin Kebbi: Na farko dai abin da zan yi kira ga al’ummar kasar nan shi ne kada su yarda da kirkiro wata sabuwar kungiyar siyasa kamar yadda Obasanjo ke bukata shi da sauran magoya bayansa. Game da abin da Obasanjo ya rubuta a cikin wasikar da ya aike wa Shugaba Buhari, na farko dai shi kansa ya tuna ’yan Arewa sun yi masa rawar gani domin a lokacin yana cikin kurukuku ’yan Arewa ne suka fito da shi daga cikin gidan yari suka wanke shi suka daure masa gida har ya zama Shugaban kasa na farar hula. A lokacin sai aka ce duk kasar nan babu wanda zai fito takarar Shugaban kasa sai Obasanjo da Olu Falae. Wadannan mutane ba su kadai ba ne a Najeriya, kuma ba su kadai ne za su iya wannan takara ba, amma haka aka zuba ido aka fara kafa wannan dimokuradiyya da son zuciya, saboda wai don a dinke barakar da ta taso sakamakon soke zaben Abiola na 12 ga watan Yuni.
Wannan shi ne ya fara jefa mulkin dimokuradiyya a cikin wani mawuyacin hali a Najeriya, domin da dimokuradiyya ta gaskiya aka kafa, wadanda suka fi yawa su ne duk abin da suka zaba za a bi. Don haka aka ci gaba da samun matsala saboda son ran wadansu. Saboda haka Obasanjo ya tuna a lokacin da yake son ya koma karo na biyu gwamnonin Arewa a karkashin jagorancin marigayi tsoho Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abdulkadir Kure (Allah Ya gafarta masa), ya jagoranci gwamnonin zuwa wurin Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar cewa sun amince Obasanjo ya dawo karo na biyu, kuma a lokacin Atiku Abubakar yana bukatar ya fito takara, amma gwamnonin Arewa suka taka masa birki, lokacin yankinsa na Yarbawa babu PDP sai dai AC.
Cif Obasanjo ya ce Shugaba Buhari yana da kabilanci, to ina son ya tuntubi dan uwansa Ministan Ayyuka da Gidaje da Wutar Lantarki, Cif Babatunde Fashola ya nuna masa yawan ayyukan da gwamnatin Buhari ta yi. Idan ya duba zai ga mafi yawan ayyukan da Buhari ya yi yana Kudancin kasar nan ne da kuma Yammaci, kuma ya sani yawan masu manyan mukamai a cikin wannan gwamnati mutanensu sun fi yawa, to ta ina ne Buhari ya nuna musu kabilanci?
Mutane suna maganganu cewa duk wanda Obasanjo ya rubuta wa wasika ba ya kai labari, to Obasanjo ya sani daga yanzu ya kai karshen rubuta wasika ga wani Shugaban kasa a Najeriya. Dalili kuwa saboda duk wadanda ya rubuta in sun yi tasiri, to wannan ba ta yin tasiri, ya tuna Jam’iyyar PDP ba irin sharrin da ba ta yi wa Buhari ba, amma da Allah Ya kawo karshenta da zabe ya zo ba wai Buhari ba, duk wanda ya tsaya bayan Buhari komai lalacewarsa ya ci zabe. Saboda haka duk mai bin Buhari da sharri ya hakura sai lokaci ya yi, domin bai dogara da kowa ba sai Allah, ba ya da wani maigida a siyasa sai Allah.
Duk take-taken Obasanjo da muguwar manufarsa a kan Buhari ba za ta samu nasara ba, kalaman Obasanjo suna nunawa a fili yadda almundahana ke kokarin dawowa da karfinta. Obasanjo yana so ne ya maye gurbin Buhari da yaron gidansa da zai rika juya shi yadda yake so, don haka Shugaba Buhari ya yi watsi da shi ya sake tsayawa takara a badi, jama’a ke da damar zaben shugabannin kirki ba Obasanjo ba. Obasanjo na so ya ga Buhari cikin shekara biyu da rabi ya daidaita Najeriya bayan shi da yaransa sun shekara 16 sun kasa ko yana bukatar Najeriya ta sake hargitsewa ne kawai?
Lallai Shugaban kasa Buhari ya san cewa mafi yawancin azzaluman kasar nan har yanzu ba sa tare da shi, amma Allah Ya ga dama Ya ba shi mulkin kasar nan. Kuma har yanzu wadannan azzalumai ba sa tare da shi, suna nan suna ci gaba da yi masa zagon kasa. Sun yi duk kokarin da za su yi domin su raba shi da talakawan Najeriya, amma saboda talakawan Najeriya suna tare da shi ba su samu nasara ba.
Aminiya: Me za ka ce game da rikicin Fulani makiyaya da manoma da ke faruwa musamman a Jihar Binuwai?
danmalikin Kebbi: Ba komai ne ba, illa iyaka wata hanya ce ta cin mutuncin Shugaba Buhari, ganin cewa shi Bafillace ne, bari a bi wannan hanya a nakasa mulkinsa. Tunda ya yi maganin Boko Haram bari a biyo masa ta wata hanyar. Wadannan kashe-kashe da suke faruwa ba komai ne ba illa siyasa ce, an kuma gano bakin zaren sai dai su sake wani salon.