Murabus din Daurawa ta tayar da kura a Facebook

Sheikh Daurawa ya bayyana murabus dinsa cikin wani faifan bidiyo.

Murabus din Daurawa ta tayar da kura a Facebook

Sheikh Aminu Daurawa

Murabus din Babban Kwamandan Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ta bar baya da kura a kafar sadarwa ta Facebook.

Wannan na zuwa ne, bayan da Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta.

Mutane sun shiga kiranye-kiranye ga Sheikh Daurawa da ya sauka daga mukaminsa, biyo kalaman gwamnan don tsira da mutuncinsa.

Shugaban hukumar dai, ya sanar da murabus dinsa da sanyin safiyar ranar Juma’a, cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A’isha Idris Madubi wata mai amfani da Facebook, ta ce: “Murabus ɗin Daurawa zai shafi gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ko ina ma. Musamman wajen aiki da gaskiya ba tare da karbar cin hanci ba”.

Usman Ahmad kuma: ya ce “Mu fa abin da ya sa ba za mu taba yin wannan tafiyar ba kenan. Sheikh Daurawa ka fi mana duk wani dan siyasa. Allahu ya sa haka shi ne mafi alheri”.

Aliyu Yakubu Yusuf, malami a Sashen Nazarin Harshen Turanci da Dab’i a Jami’ar Bayero ta Kano, cewa ya yi, “Subhanallah! Wallahi ban so Sheikh Aminu Daurawa ya ajiye muƙaminsa na shugaban Hisba ba. Amma wannan shi ne hukuncin da ya yanke, kuma dole kowa ya yarda. Allah ya sa hakan ya zama alheri a gare shi da kuma Kanawa. Allah Ya ɗaukaka addinin Musulunci da Musulmai a ko ina a Duniya. Allah Ya shirye mu baki ɗaya.”

Muhammad Saddik ya ce “Amma bai kyauta ba gaskiya. A matsayinsa na malami mai kokarin gyara da sulhu, idan ya saurari ’yan hana ruwa gudu masu zuga shi, shi kenan kuma sai a bar gwamnati ta lalace! Kenan malami bai zama mai hakuri ba kenan bai dauki nasihar shugaba SAW ba?

“Duk ɗan Kwankwasiyya yana Allah wadai da wannan matakin da Gwamnatin Kano ta dauka na fadakar da Hukumar Hisbah, kowa yana son nasiha kuma kowa mai iya yin nasiha ne, Hukumar Hisbah tana da nata kuskuren amma a matsayinta a cikin al’umma wannan sigar ba ta dace da yi mata nasiha ba.

“Allah Ya bi awa malaminmu Daurawa hakuri don Allah ya dawo ya ci gaba da abin da ya fara”.

Wani magoyin bayan Gwamnan Jihar Kano kuma dan ɗarikar kwankwasiyya, Yushaa Abdullah Musa, cewa ya yi: “Da ni ne Daurawa 2027 takarar gwamna zan fito a Kano.”

Shi kuwa Sir Concept Me Zuma, cea ya yi “Shi ma dai malam ya yi sauri… Ita duniya mun zo zaman jarrabawa ne… Allah ne ya jarrabe ka… da ka yi hakuri. Ko wane aiki akwai kalubale.”

Wannan tirka-tirka ta samo asali ne, tun bayan da hukumar Hisbah a jihar ta kama fitacciyar ‘yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, tare sa gurfanar da ita a gaban kotun Musulunci.

Daga bisani Murja ta fice daga gidan yari, lamarin da ya sanya wasu ke ganin matashiyar na da uwa a gindin murhu a gwamnatin jihar.

Sai dai Kwamishinan Yada Labaran jihar, Baba Dantiye, ya musanta zargin da ake yi na hannun gwamnatin jihar na fitar da ita daga gidan yarin.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano