Murar tsuntsaye ta jawo asara a Kamaru

Sakamakon bullar cutar murar tsuntsaye  a kasar Kamaru, gwamnati ta yi asarar CFA biliyan 66 a gonar kajin Mbog-Betsi, inda jami’an kiwon lafiya suka bayyana cewa a nan cutar ta samu asali.Rahotanni sun ce kaji kusan dubu 15 ne suka harbu da murar tsuntsaye, kuma hukumomi daga bisani sun hallaka guda dubu 33 da gonar […]

Murar tsuntsaye ta jawo asara a Kamaru
Murar tsuntsaye ta jawo asara a Kamaru

Sakamakon bullar cutar murar tsuntsaye  a kasar Kamaru, gwamnati ta yi asarar CFA biliyan 66 a gonar kajin Mbog-Betsi, inda jami’an kiwon lafiya suka bayyana cewa a nan cutar ta samu asali.
Rahotanni sun ce kaji kusan dubu 15 ne suka harbu da murar tsuntsaye, kuma hukumomi daga bisani sun hallaka guda dubu 33 da gonar kajin ta kunsa.  
Wannan lamari ya jefa dimbin ’yan kasuwa cikin halin ni-’yasu dalilin haramta sayar da kaji a duk fadin birnin Yaounde da hukumomi suka yi.
Hakan ya sanya ‘yan kasuwar kaji yin tagumi a  kasuwanni, inda suke jiran tsammani. Har ila yau, hukumomi sun bayyana cewa duk wani wanda aka samu da laifin sayar da kajin ko da a boye ne zai biya tara. Wannan ya sa ’yan kasuwar yin korafi game da rashin samun damar tafiyar da kasuwancinsu, alhalin kamar yadda suka ce cutar ba ta bazu a duk fadin birnin Yaounde ba, face a a wuri guda da aka riga aka killace.
A nata bangaren, gwamnati cewa take daukar matakan  rigakafi ne ga dakile bazuwar cutar.
Zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu wani bayani game da tsawon wa’adin haramcin cinikin kajin. Hakazalika, babu wata diyyar da gwamnati ta ce za ta biya wadanda asarar ta shafa.
Kodayake, a wasu unguwanni masu cikin gasassun kaji suna ci gaba da tafiyar da harkokinsu.