MURIC Ta Yi Tir Da Taron INEC A Coci
Kungiyar Kare Muradun Musulmi a Najeriya (MURIC) ta yi Allah wadai da taron da Hukumar Zabe na Legas (INEC) ta shirya gudanarwa a Cocin Ikeja da ke Jihar Legas.
Kungiyar Kare Muradun Musulmi a Najeriya (MURIC) ta yi Allah wadai da taron da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta shirya gudanarwa a Cocin Ikeja da ke Jihar Legas.
Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya ce bai dace ba INEC ta shirya taro, amma ta rasa inda za ta gudanar da shi sai a wurin bautar wani addini.
- Masu shigo da jabun magunguna Kano sun gurfana a Kotu
- 2023: Ba mu da dan takara a Najeriya —Birtaniya
“Wannan abin kunya ne! Me zai sa Hukumar Zabe, wadda ta al’ummar Najeriya ce baki daya, amma ta ware addini guda ta ce a wurin bautar mabiyansa za ta yi taro? Wannan ba daidai ba ne!
“Ba boyayyen abu ne ba a Najeriya cewa fasto-fasto sun tsoma kansu cikin siyasa, har sun maida zaben 2023 tamkar wani yaki tsakaninsu da Musulmi; Don haka akwai ayar tamabya a wannan lamari na INEC. Duk Legas ba wurin taro ne sai a coci?
“Muna kira ga al’ummar Legas da babbar murya da su sanya ido sosai kan Hukumar Zaben daga yanzu, domin mun fara cire tsammanin za ta gudanar da adalin zabe,” in ji Akintola.
Da haka ya ja hankalin Hedikwatar INEC ta kasa ta ja kunnen reshenta na Jihar Legas, domin guje wa nuna bangaranci.