Murja: Sheikh Daurawa bai yi murabus ba —Hukumar Hisba
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da cewa har yanzu Babban Kwamnadanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa na nan kan kujerarsa bai yi murabus ba.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da cewa har yanzu Babban Kwamnadanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa na nan kan kujerarsa bai yi murabus ba.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar, Sheikh Mujahid Aminuddeen Abubakar ne ya sanar da hakan.
Sheikh Mujahid ya bayyana haka ne bayan rade-radin da ke yawo cewa Sheikh Daurawa ya yi murabus, kan takaddamar sakin jarumar tiktok, Murja Ibrahim Kunya, daga gidan yari, bayan kotun Musulunci a ba da umarnin tsare ta.
A ranar Lahadi Aminiya ta ruwaito cewa an fitar da Murja daga gidan yari, sabanin umarnin kotu, lamarin da ya haifar da damua a cikin al’umma.
- Yau za a ci gaba da shari’ar Ramlat ’yar TikTok
- Kuncin Rayuwa: Yadda Trust Radio Ya Faranta Ran Masoya a Abuja
Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gama PRP a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare matashiyar a gidan yari ne ba bayan hukumar hisbah ta gurfanar da ita kan zargin karuwanci ga kananan yara, da kuma badala, zargin da ta musantarbiyya.
Alkalin kotun, Mai sharia Nura Yusuf Ahmad, ya bayar da umarnin tasa keyarta zuwa gidan yari tare da dage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu, 2024.
‘Alkali bai da belin Murja ba’
Muzammalin Ado, kakakin kotunan Musulunci a Jihar Kano, ya ce kotu ba ta ba da belin Murja ba.
A cewarsa, a lokacin da aka tashi a kotu, “Alakli ya ce za dawo domin ya yanke hukunci kan bukatar neman belinta; ba zai yiwu a canza abin da aka yi a cikin zauren kotu ba.
“Mu abin da muka sani shi ne Murja tana gidan yari, kamar yadda yake a shari’a.”
Da umarnin kotu muka sake ta —Gidan yari
Amma a bangarensa, kakakin gidan gyaran na Kurmawa, Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ya ce sun saki Murja ne tun a ranar Alhamis bayan da suka samu takardar umanin kotu a game da hakan.
“Takarda ce ta kawo Murja, kuma takarda ce ta fitar da ita,” in ji shi.
A cewarsa, “Gidan yari na tafiya ne bisa dokoki, kuma dukn wanda aka tsare a gidan yari takarda ce take kai shi da sa hannun alkali, kuma takarda ke fitar da shi da sa hannun alkali.
“Muna da sa hannun dukkanin alkalan da ke Jihar Kano, dole sai alkali ya sa maka hannu sannan za a kawo ka, haka ma dole sai ya sa hannu kafin a fitar da kai.
“A takaice kotu ce ta kawo Murja, ita ce kuma ta fitar da ita.”
Hurumin hukumar Hisbah
Hukumar Hisbah, wadda ta kama Murja, ta ce ita aikinta shi ne ta kama mutum, amma ba ta da hurumi kan yanke masa hukunci ko fada wa alkali irin hukuncin da zai yi masa.
Haka kuma Hisba ta ce wannan abu da ya faru ba zai sa ta yi kasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.
Al’umma dai na ci gaba da lugudan labba musamman a shafukan sada zumunta kan wannan lamari.