Murja ta kai ƙarar Hisbah gaban Kotu

Lauyoyin Murja sun gabatar wa Babbar Kotun Jihar Kano buƙatu bakwai.

Murja ta kai ƙarar Hisbah gaban Kotu

Murja Kunya

Fitacciyar jarumar nan ta dandalin TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta yi ƙarar Gwamnatin Kano a gaban Babbar Kotun jihar.

Wannan dai na cikin ƙunshin takardar ƙarar da Murja ta shigar bisa wakilcin lauyoyinta — A. U Hajji da S.S Shehu — mai ɗauke da kwanan watan 26 ga Fabarairun 2024.

A ƙunshin ƙarar da Magatakardan Kotun, Adam S. Adam ya rattaba hatimi da kuma sa hannu, Murja ta buƙaci a shiga tsakaninta da Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kwana Huɗu.

Aminiya ta ruwaito cewa, cikin jerin waɗanda ƙarar da Murja ta shigar ta shafa akwai Antoni-Janar na Jihar Kano da Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, da Hukumar Hisbah da Hukumar Asibitocin Kano da Babban Asibitin Masu Larurar Kwakwalwa da ke Dawanau.

Takardar ta nuna cewa, Babbar Kotun ta cimma muradu huɗu daga cikin jerin buƙatu bakwai da lauyoyin Murja suka gabatar wa Mai Shari’a Nasiru Saminu.

Sai dai Aminiya ta lura cewa, daga cikin buƙatun lauyoyin Murja da kotun ta yi watsi da su, har da ta neman mayar wa wadda suke wakilta wayarta ta hannu kirar iPhone da kuma katin banki na ATM.

Da wannan hukuncin ne kotun ta kuma ɗage ƙarar zuwa 20 ga watan Maris na 2024.

Ana iya tuna cewa, a bayan nan dai Mai Shari’a Malam Nura Yusuf Ahmad na Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kwana Huɗu ya bayar da umarnin a yi wa Murja gwajin kwakwalwa.

Mai Shari’a Nura Yusuf ya ba da umarnin yi wa Murja gwajin kwakwalwar ne a asibitin gwamnati domin tabbatar da ƙoshin lafiyarta

Alkalin ya ba da umarnin ne bisa zargin jarumar ba ta cikin hayyacinta a lokacin zaman kotun na farko da aka gurfanar da ita.

Tun farko dai Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce ta gurfanar da Murja kan zargin tayar da hankalin jama’a, bata tarbiyya da kuma koyar da karuwanci.

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele